Dandalin WhatsApp ya raba kayan abinci na sama da Naira miliyan 5 ga mabuƙata a Katsina

Wata gidauniya da ke ƙarƙashin wani Zauren WhatsApp mai suna Katsina City News, ta tara kuɗi har Naira miliyan biyar da dubu ɗari ɗaya da sha bakwai, inda inda ta riƙa taimakon mabuƙata a lokacin Azumin watan Ramadan.

Zauren na WhatsApp wanda na ‘yan Jihar Katsina da suka fito daga mabambantan jam’iyyun siyasa da ra’ayoyi daban-daban, sun haɗu ƙarƙashin inuwa ɗaya domin ci gaban Jihar Katsina.

Kwamitin Azumi da Zauren ya kafa ƙarƙashin shugabancin tsohon Shugaban Ma’aikata na Jihar Katsina, Alhaji Lawal Aliyu Daura mni, yana da membobi da suka haɗa da Hajiya Mariya Abdullahi Bakori, Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina, Alhaji Lawal Rufa’i Safana, Alhaji Dauda Kurfi, Hajiya Murja Saulawa, Barista Ahmad Danbaba Batsari. Alhaji Muntari Lawal Kofar Soro, Alhaji Hamza Yunusa Jibia, SSA Sabo Musa Hassan da sauran su.

Wannan ita ce shekara ta huɗu da wannan kwamitin ke aikin sa duk lokacin Azumin watan Ramadan.

A bana, kwamitin ya bai wa gidajen mabuƙata 500 abinci da kuɗin cefane. Inda kowane gida ya samu shinkafa, garin masara, taliya, magi da man girki da kuma kuɗin cefane.

Haka nan, Kwamitin ya kuɓutar da matasa bakwai daga gidan yari bayan ya biya masu ‘yan ƙananan tara, ya kuma biya wa mata 20 ƙananan tara na bashi da aka kai su kotu a kai.

Kwamitin ya kuma riƙa kai abinci dafaffe a gidan baƙi da asibiti domin marasa lafiya da akan kawo daga karkara ba su da kowa a cikin Katsina.

Kuɗaɗen da ake wannan aikin, ‘yan zauren ke tarawa a tsakaninsu.

Mawallafin jaridur yanar gizo ta Katsina City News da mujjalar Katsina City News, Muhammad Danjuma, shi ne wanda ya ƙirƙiri wannan zaure a 2015.

Kuma ya haɗo kan mutane daban-daban ‘yan Katsina domin musayar labarai da tattauna abin da ya shafi Jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.

Zauren ya saba kai ɗauki na kuɗi da sauransu ga jama’a da iftila’i ya shafa a Katsina.