Dangantakar Ƙasar Sin da Taiwan tamkar ta uba ne da ɗansa

Daga FA’IZA MUSTAPHA

Wasu mutane na ƙoƙarin kwatanta rikicin Ukraine da Rasha da batun yankin Taiwan na ƙasar Sin. Amma abun da mutane da yawa ba su fahimta ba, batutuwan biyu sun sha bambam da juna.

Ukraine ’yantacciyar ƙasa ce mai cin gashin kanta a yanzu haka, haka ma ƙasar Rasha, don haka, rikicin dake tsakaninsu, rikici ne na ƙasashe maƙwabta, yayin da Taiwan tun fi azal, ke kasancewa wani yanki na ƙasar Sin dake ƙarƙashin ikonta.

Yayin da rikicin Rasha da Ukraine ke mayar da hankali kan tsarin tsaro a nahiyar Turai, batun Taiwan ya shafi cikin gidan ƙasar Sin ne. Misali, kamar uba ne da ’ya’yansa, sai wani daga can waje ya ce zai jagoranci yadda ya kamata magidanci ya tarbiyantar ko tafiyar da harkokin ’ya’yansa.

A ganina, babu wani uba da ya san ciwon kansa, da zai bari ana tsoma baki cikin harkokin cikin gidansa ko kuma a nemi nuna masa fin ƙarfin kana abun da yake mallakinsa. Tun asali, Taiwan ba ƙasa ba ce, yanki ne a cikin ƙasar Sin, don haka, jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin ce ke wakiltar ta a matakin ƙasa da ƙasa.

Ban da wannan, atisayen da sojojin ’yantar da al’ummar ƙasar Sin ke yi a tekun kudancin ƙasar, ba matakan soji na yaƙi ba ne, tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro, tare kuma da bayyana ƙarfin ƙasar Sin na dakile duk wata barazana dake neman ta da rikici a yankunanta ko kawo cikas ga kwanciyar hankalin ɗaukacin ƙasar.

Don haka, duk wani mataki da ƙasar ta ɗauka dangane da batun, ta ɗauke shi ne bisa doron doka, kamar yadda haƙƙin tsawatarwa ya rataya a kan uba, haka ya kamata ƙasar Sin ta tsawatarwa Taiwan har ma da masu goya masa baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *