Dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha ta sha bamban da dangantakar da ke tsakanin Amurka da sauran wasu ƙawayenta

Daga CRI HAUSA

A yayin da take mayar da martani ga kalaman mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price, dake alakanta da ƙasar Sin da batun Ukraine, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a yau Alhamis cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, ta dogara ne kan ra’ayin ba ruwanmu, ba nuna adawa, kana ba za ta goyi bayan hari kan bangare na uku ba, wanda hakan ya sha bamban da yadda Amurka ke yi, ta hanyar kafa “kananan kungiyoyi” bisa bambancin ra’ayi, da rura wutar adawa da rarrabuwar kai.

Hua ta ƙara bayyana cewa, game da batun yadda za a mutunta mulkin kan ƙasa, da kuma cikakken yankin ƙasa, Amurka ba ta cancanci ta gaya wa ƙasar Sin abin da ya kamata ta yi ba. Ta ce jama’ar ƙasar Sin suna da ainihin fahimta kan mulkin kan ƙasa, da kuma cikakken yankin ƙasa.

Baya ga haka, Hua ta nuna cewa, a cikin ƙasa da shekaru 250 da kafuwar ƙasar Amurka, shekarun da ta shafe ba ta gudanar da ayyukan soji a ƙasashen waje ba sun kai 20. Har kullum ta kan fake da dalilai na kare dimokuradiyya, ko hakkin dan adam wajen kaddamar da yaki, har ma a wasu lokutan dalilan nata ba sa wuce karamar kwalbar hoda, ko kuma labarin karya.

Game da maganar Amurka a fakaice, cewa wai ƙasar Rasha ta dauki mataki ne saboda goyon baya da ta samu daga ƙasar Sin, Hua ta bayyana cewa, Rasha mamba ce ta dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kuma ƙasa ce mai cin gashin kanta, kuma ɓangaren Rasha yana tsarawa, da aiwatar da dabarun diflomasiyya bisa ga matsayar ƙasar da muradun ta.

Fassarawa: Bilkisu Xin