Daga FA’IZA MUSTAPHA
Ƙasashen Afrika na kara samun ci gaba da ƙara amfana daga kyakkaywar dangantakar moriyar juna dake tsakaninsu da ƙasar Sin.
A wannan mako, ƙasar Habasha ta ƙaddamar da manyan ayyukan ci gaba guda biyu masu muhimmanci ga tattalin arziki da walwalar jama’a da suka hada da yankin ciniki cikin ’yanci na farko a ƙasar da kuma wani babban titin da ya fara daga shataletalen Alexander Puskin zuwa babban titin Gotera, dake birnin Addis Ababa.
A ko da yaushe, na kan ce dangantakar Sin da ƙasashen Afrika dangantaka ce ta zahiri da idanu ke iya gani, sannan al’umma kan amfana kai tsaye.
Yankin masana’antu na Dire Dawa da tashar jiragen ruwa ta kan tudu da tashar jirgin ƙasa da ta haɗa Habasha da Djibouti ne suka haɗe, suka zama yankin na ciniki cikin ’yanci.
Dukkan waɗannan ayyuka ne da Sin ke da ruwa da tsaki wajen wanzuwarsu, waɗanda kuma ƙasar za ta daɗe tana cin gajiyarsu.
Yankin masana’antu na Dire Dawa kaɗai, zai taimaka wajen samar da ayyukan yi na kai tsaye da wanda ba na kai tsaye ba ga al’ummar ƙasar 40,000, baya ga waɗanda ya samarwa aikin yi yayin da ake gininsa. Wannan yankin da ba za a taba raba nasararsa da taimakon ƙasar Sin ba, zai yi gagarumin taimako wajen haɓaka cinikayya tsakanin kasar da sauran ƙasashen Afrika musamman na gabashin nahiyar da sauƙaƙa jigilar kayayyaki da inganta rayuwar mazauna yankin da ma kai ƙasar ga cimma burinta na zama ƙasa mai matsakaicin kuɗin shiga zuwa shekarar 2025.
Ƙasar Habasha ta tsara burinta na zama cibiyar samar da kayayyaki da masana’antu na zamani a nahiyar Afrika, kuma ƙasar Sin tana iya ƙoƙarinta na ganin ta cimma wannan buri.
Har ila yau a jiya, ƙasar ta ƙaddamar da babban titin da ya fara daga shataletalen Alexander Puskin zuwa babban titin Gotera, a birnin Addis Ababa.
Titi muhimmin aikin more rayuwar al’umma ne domin zirga-zirga ya shafi dukkan ɓangarorin rayuwa, kama daga zuwa aiki, asibiti, jigilar kayayyakin buƙata, da dai sauransu. Tabbas ƙasar Sin ta cancanci yabo.
Haƙiƙa duk wanda zai soki dangantakar Sin da Afrika, to ba ya kaunar ganin ci gaban ƙasashen na Afrika, domin cikin lokaci kalilan da aka ɗauka na dangantakar ɓangarorin biyu, an samu dimbin nasarorin da suka amfanawa daukacin al’umma, waɗanda tarin zuri’a masu zuwa, su ma za su ci gajiya.