Dangin ‘yan siyasa na wawashe asusun Nijeriya – Hukumar FIRS

Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS) ta bayyana cewa, dangin ‘yan siyasar ƙasar nan ke wawushe kuɗaɗen harajin da ake tara wa ƙasa.

Bayanin haka ya fito fili ne a lokacin da wasu ma’aikatan hukumar suka bayyana tsoron makomarsu idan ya zamana cewa ikon karɓar haraji ya fita daga hannun hukumar ya koma hannun jihohin ƙasar nan.

Da alama dai ‘yar tsamar da ke tsakanin hukumar tara haraji ta FRIS da wasu jihohin ƙasar nan kan batun ikon karɓar haraji na ci gaba da zafafa ganin cewa ana samun ƙarin jihohin da ke ra’ayin su ma a ƙyale su su karɓi harjinsu da kansu, kamar dai yadda jihar Ogun da Akwa Ibom suka ce a shirye suke su kafa dokar da za ta ba su damar karɓar haraji da hannunsu.

Wannan al’amari dai ya sa tuni cikin wasu ma’aikatar FIRS ya ɗuri ruwa wanda a bisa hange da hasashensu, muddin karɓar harajin ya koma hannun jihohi hakan ba zai haifar musu da ɗa mai ido ba.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, wasu ma’aikatar FRIS sun shaida mata cewa karɓe ikon tara haraji daga hannun hukumar FIRS hakan zai rage yawan kuɗaɗen da ya kamata a ce hukumar ta tara da Naira biliyan 96.

A cikin wata takarda da FIRS ta gabatar wa Majalisar Tarayya, ta yi hasashen tara kuɗaɗe har Naira tiriliyan N2.44 ya zuwa 2022 ta ɓangaren kayayyakin da ake shigowa da su cikin ƙasa da waɗanda ake fitarwa.

Don haka ta ce idan kuwa aka sake ikon karɓar harajin ya koma hannun jihoji, babu shakka za a tafka hasarar waɗannan kuɗaɗe kamar dai yadda wata majiya daga hukumar ta shaida wa Punch.

Majiyar ta ci gaba da cewa, ɓangaren fetur shi ne wauri mafi girma da hukumar ta fi tara haraji, sai kuma ta hannun kamfanoni da ‘Stamp Duty’ da dai sauransu.

Ta ƙara da cewa, “Muddin muka daina karɓar haraji, FIRS ba za ta iya ci gaba da ɗaukar ɗawainiyar ma’aikatanta ba. Hasali ma, da damanmu a tsorace muke don kuwa ba mu san abin da zai faru a gaba ba.”

Wani jami’i a hukumar FIRS ya shaida wa jaridar Punch cewa, “Babbar matsalarmu a FIRS ita ce kusan kowane ɗan siyasa mai ƙumbar susa a ƙasar nan yana da wani nasa a hukumar saboda yadda harkoki ke gudana a ƙasar nan ta yadda akan bai wa ‘yan siyasar damar ɗaukar aiki.

“Matsalar ita ce, muna da ma’aikata da yawan gaske wanda ake kashe kuɗaɗe masu yawa wajen biyan albashinsu da sauran dawainiyarsu. Ba ƙaramar sa’a ba ce idan wasunmu ba su rasa aikinsu ba a ƙarshen lamari.”

Bayanai sun tabbatar da cewa daga cikin kason Naira biliyan N216.65 na FIRS na 2021, an ware Naira biliyan 107.52 ne don kula da ma’aikata, biliyan N47.22 don gudanar da harkokin hukumar, sannan biliyan N61.9b don manyan ayyukan hukumar.

An ce ya zuwa 2019, FIRS na da ma’aikata da yawansu ya 9,000 wanda akwai yiwuwar adadin ya ƙaru ya zuwa yau.

An zargi hukumar da kashe kuɗaɗe barkatai da suka haɗa da ware miliyan N160 don ɗinka wa direbobinta su 850 rigar aiki, miliyan N825 don shaƙatarwar ma’aikata, miliyan N250 don sha’anin tsaro da dai sauransu.