Dangote ya kusa ƙaddamar da katafariyar matatar mai a Legas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ana sa ran Kamfanin Matatar Man Fetur na Dangote na biliyoyin daloli zai kawo mafita ga al’amuran matatar mai a Nijeriya.

An ruwaito wata majiya ta bayyana cewa, shugaba Buhari zai ƙaddamar da kamfanin.

A baya dai, kamfanin Dangote ya yi nuni da cewa, za a ƙaddamar da matatar man a Legas kafin ƙarshen wa’adin mulkin shugaba Buhari a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin Dangote, Mista Anthony Chiejina, a wata sanarwa da ya fitar ya ƙaryata rahotannin da ke cewa matatar na daga cikin ayyukan da Buhari zai qaddamar a ziyarar da ya kai Legas a watan Janairu.

“Duk da haka, za a ƙaddamar aikin matatar manmu kafin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki a watan Mayun 2023, kuma za a sanar da jama’a yadda ya kamata a gayyace su zuwa wurin taron,” in ji kamfanin a cikin sanarwar.

Katafaren matatar man Dangote da ke unguwar Lekki Free Zone a Legas, ya mamaye fili kimanin hekta 2,635, wanda ya fi girman tsibirin Victoria Island a Legas.

Matatar man ita ce matatar mai mafi girma a Afirka sannan kuma ita ce matatar jirgin ƙasa da ya mafi girma a duniya.

Bayan kammala aikin matatar man ana sa ran za ta cika kashi 100 cikin 100 na abin da Nijeriya ke buƙata na dukkan kayan da aka tace sannan kuma ta samu rarar kowanne daga cikin waɗannan kayayyakin don fitar da su zuwa ƙasashen waje.

Matatar dai an yi ta ne domin sarrafa ɗanyen man Nijeriya kuma tana iya sarrafa sauran ɗanyen mai.

Aikin biliyoyin daloli ne da zai samar da kasuwa na dala biliyan 21 a duk shekara na ɗanyen man Nijeriya.