Dangote zai mayar wa kwastomomin da suka sayi fetur da tsada kuɗinsu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matatar mai ta Dangote ta bayyana shirin mayar wa kwastomomin da suka sayi man fetur a farashi sama da farashin da ta ke bayar daga manyan dillalai kuɗaɗen su.

Sanarwar ta zo ne bayan da matatar man ta rage farashin man fetur a kwanan baya daga N890 zuwa N825 a kowace lita.

A cewar sanarwar da aka fitar a ƙarshen makon nan, kamfanin zai mayar da Naira 65 kan kowace lita fiye da tan 200,000 na man fetur da ‘yan kasuwa suka saya a kan tsohon farashi kafin a fara aiwatar da ragi.

“Matakin, wanda ya fara aiki a ranar 27 ga Fabrairu, 2025, ya ba da tabbacin cewa babu wani abokan kasuwancinmu masu Dangote da zai fuskanci asara saboda canjin farashin. Mafi muhimmanci, yana tabbatar da cewa sabon ragin ya fara aiki nan take a duk faɗin ƙasar don amfanin al’ummar Nijeriya,” inji kamfanin.

Matatar ta tabbatar da cewa ta yi asarar Naira biliyan 16 ta hanyar samar da waɗannan kuɗaɗen, inda ta jaddada cewa matakin ya yi daidai da ajandar sabunta Nijeriya na Shugaba Bola Tinubu, da ke da nufin haɓaka tattalin arziki.

Dangote ya yi Allah wadai da duk wani amfani da sabon tsarin farashin da ‘yan kasuwa ke yi. “Ba abin kishin ƙasa ba ne, kuma yana yin illa ga rayuwar ‘yan Nijeriya, domin duk wanda ya saya a kan Naira 825 kan kowace lita sannan ya sayar wa masu amfani a kan Naira 945 ko fiye da haka, wannan ya cin riba ns fiye da kima,” inji sanarwar.

Kamfanin ya wallafa farashin da aka amince da shi ga manyan abokan hulɗar sa: MRS zai sayar a kan N860 a Legas, N870 a Kudu maso Yamma, N880 a Arewa, N890 a Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. Heyden da AP (Ardoɓa Plc) za su sayar a kan N865 a Legas, N875 a Kudu maso Yamma, N885 a Arewa, N895 a Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.

Tare da wannan farashin, Dangote yana tsammanin babu wani ɗan Nijeriya da zai biya fiye da Naira 900 a kowace lita.

Matatar matatar ta jaddada ƙudirinta na samar da man fetur mai inganci wanda zai amfanar da ayyukan ababen hawa da kuma tallafawa lafiyar al’umma tare da bayar da gudunmawar samar da makamashi da ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.

“Wannan shiri yana ɗaya daga cikin hanyoyi da dama da matatar man Dangote ke ci gaba da ba da gudunmawa don samun ci gaba mai ɗorewa ga ƙasarmu,” inji kamfanin.