Dangut ya zama Shugaban WAEC na ƙasa

An naɗa Dokta Amos Dangut a matsayin sabon Shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare a Afrika ta Yamma (WAEC) a Nijeriya.

Kafin naɗin nasa, Dangut shi ne Mataimakin Rijistara na WAEC na ƙasa.

Naɗin nasa ya biyo bayan ƙarewar wa’adin aikin Mr Patrick Areghan a matsayin shugaban hukumar na ƙasa.

Bayanin naɗi na ƙunshe ne cikin sanarwar da WAEC ta fitar ranar Litinin ta bakin Mrs Moyosola Adesina wadda ta kasance Muƙaddashin Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a hukumar a Legas.

Adesina ta bayyana cewa, Dangut ya fara aiki da hukumar ne a shekarar 1998 ne a matsayin “Assistant Registrar (AR) II”, sannan ya zama “Deputy Registrar” a Afrilun 2018.