Daraja da girmamawar da ake bai wa mawaƙa ba ta kai yadda ake buƙata ba – Tijjani Gandu

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A satin da ya gabata, mun faro firarmu da neman sanin ko waye mawaƙi Tijjani Gandu, kafin mu garzaya kan dalilin tattaunawar tamu, wato waƙoƙi, inda ya yi mana bayyanin yadda ya faro da kuma yadda ya sauya akalan waƙoƙinsa daga na soyayya da kuma yabon fiyayyen halitta zuwa na siyasa, da ma wanda ya zama silar faruwar hakan. Kamar yadda muka yi alƙawarin kawo maku ci gaban wannan tattaunawa, Allah Ya kawo mu, lokaci ya yi, don haka a sha karatu lafiya.

MANHAJA: Shin kana ganin ýan siyasa na rama wa kura aniyarta, ganin irin rawar ganin da ku ke takawa wajen sanya soyayyar su a wajen jama’a da tallata manufofin su?

TIJJANI GANDU: Gaskiya ba tun yanzu ba, daraja da girmamawar da ake bai wa mawaƙi ko mawallafi ba ta kai yadda ya ake buƙata ba. Wasu na ganin mawaƙi kamar maroƙi ne kawai, ko ɗan maula, don haka ba kasafai ake ba shi muhimmanci sosai ba. Ita kuwa waƙa ba abin banza ba ce, don komai kuɗinka, sai Allah ya yi maka baiwar ƙirƙira. Ina ganin wannan riƙon sakainar kashin da ake yi wa mawaƙa ya samo asali ne tun a shekarun baya, saboda yadda mawaƙan da suka gabata suka ɗauki sana’ar. Kodayake yanzu ana samun canji, irin kulawa da karramawar da ake nuna mana ya fi na baya.

A ƙarƙashin shugabancinka wanne sauyi ka ke so ka kawo kan yadda ake ɗaukar mawaƙan Kwankwasiyya?

Muna faɗawa mambobin mu, da duk wanda muke tare da shi, da ma wanda ya zo neman shawara a kan harkar cewa, ita waqa baiwa ce, ita kuma ba saya ake ba, idan Allah ya ba mutum sai ya riƙe ta da daraja. Sai ya girmama kansa al’umma za ta girmama shi. Na farko wasu mawaƙan suna ɗaukar waqa kamar harkar roƙo ko neman abin hannun mutane. Ka yi wa mutum waƙa don cigaban harkokin sa ko siyasar sa, amma wai roƙonsa ka ke yi don ya karva, don ya baka wani abu, ka ga wannan ya zama roƙo ba sana’a ba. Muna son mawaƙan mu su ɗauka wannan harka sana’a ce babba. Idan ka riƙe mutuncinka kana addu’a, babu matakin da ba za ta kai ka ba, babu inda waƙa ba za ta kai ka ba.

Wacce gudunmawa ka ke ganin ka bayar da sauran abokan waƙar ka, wajen samun nasarar Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano?

Tun daga 2019 zuwa 2023 gudunmawar da na bayar a wannan tsarin na tafiyar Kwankwasiyya Abba Gida Gida na da yawa. Wasu na ganin na ba da gudunmawa da kaso 50 cikin ɗari, ko kaso 80 cikin ɗari, wasu ma sun ce kaso 30, amma ko ma dai yaya ne, su waɗanda ake yi don su sun sani cewa na ba da gudunmawar da ba za a iya misaltata ba.

Kai wanne maki ka bai wa kanka?

Ni ba zan iya yanke wani maki in ce zan bai wa kaina ba, don ba na son yin alfahari. Amma dai haƙiƙa na san na yi rawar gani kuma na ba da gagarumar gudunmawa, ba ni kaɗai ba da sauran ýan’uwa mawaƙa. Na sani waƙoƙina sun yi tasiri, musamman ta Abba Gida Gidan nan, tun a 2019 har zuwa wannan lokacin.

Ɗan Adam ba a raba shi da hassada ko nuna ƙiyayya ga abin da bai samu ba, kana jin a wannan harka ta waqa kana da maqiya ko masu hassada da cigaban da ka ke samu? Kuma yaya ka ke ji?

To, wani abin za a gaya maka ko za ka ji da kunnenka, ko ka gani da idonka, wani abin ma shaguɓe ne ko a gaya wa wanda ka je tare da shi. Duk wanda Allah ya yi wa ɗaukaka, ba ka raba shi da mahassada, idan ka san abin da ka ke yi wannan hassada da ƙiyayyar sai ka riqe ta ta zame maka taki. Idan ka ce kulawa za ka yi to, da kai da shi sai ku faɗi gabaki ɗaya. Dole ne rayuwa tana da wannan qalubalen, wani na baƙin ciki da ɗaukakar da ka ke ciki, yana ganin mai ya sa ba shi ne ya samu ba.

Wacce shawara za ka bai wa masu irin wannan hali?

To, dama ita hassada ai kowanne addini ka ke bata da kyau. Kuma ita hassada taki take zame wa. Duk lokacin da ka sa wani ɗan Adam kana yi masa hassada to, fa kamar kana ƙara yayyafa masa taki ne yana ƙara fitowa, musamman ma in bai kula ka ba. In ya kula ka ne ma za ka ci riba a kansa. Amma in bai kula ka ba, hassadar nan taki take zame masa. Don haka hassada ba ta da kyau, ya kamata a daina, ɗaukaka ta Allah ce.

Wanne saƙo ko shawara ka ke da shi ga sabuwar gwamnati mai zuwa a Jihar Kano?

Shawarata dai ita ce, a tsaya a yi wa al’ummar Kano abin da ya dace. Ba maganar jam’iyya ba duka al’ummar Jihar Kano suna da haƙƙi kan Abba Gida Gida. Ina fatan zai yi iya ƙoƙarinsa, mun riga da mun san akwai ƙalubale mai yawa na abubuwa da aka lalata a gwamnatin baya, amma an ce mai gyara ba ya ɓarna. Yana da dama, idan Allah ya so, bayan huɗun nan ma ya maimaita. Ina fatan kamar yadda aka nuna masa soyayya, aka zubar da hawaye a kansa, aka hana ido barci, wasu ma suka rasa rayukansu, kan Abba Gida Gida ya zama gwamna, so muke yi har ƙarshen wa’adin mulkinsa jama’ar Kano na wannan mararin da cewa, wane ɗin nan ya zo ya yi abin da ya dace. Ba ma fatan wannan soyayyar ta juya ta zama ƙiyayya, muna son ta ɗore a kan an yi abin da ya dace.

To, madalla. Na gode.

Ni ma ina godiya sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *