Darajar kayayyakin da Sin ta shigo da fitar da su zuwa ƙasashen dake aiwatar da shawarar “Ziri ɗaya da hanya ɗaya” ta kai Yuan tiriliyan 2.93 daga Janairu zuwa Maris

Daga CMG HAUSA

Yau Laraba da safe, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar ƙasar Sin ya kira taron manema labarai, inda kakakin babbar hukumar kwastam ta ƙasar, wanda kuma shi ne shugaban sashin nazarin alƙaluman ƙididdiga, Li Kuiwen ya gabatar da bayani game da harkokin shige da fice na watan Janairu zuwa Maris din bana.

Alƙaluman hukumar sun nuna cewa, a watan Janairu zuwa Maris din bana, darajar kayayyakin da ƙasar Sin ta shigo da fitar da su zuwa ƙasashen dake aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya ɗaya” ta kai kudin Sin Yuan tiriliyan 2.93, wanda ya karu da kaso 16.7 bisa ɗari, ciki har da Yuan tiriliyan 1.64 na kayayyakin da ta fitar zuwa ƙetare, wanda ya karu da kaso 16.2 bisa dari, sa’annan da Yuan tiriliyan 1.29 na kayayyakin da ta shigo da su, wanda ya karu da kaso 17.4 bisa ɗari.

Fassarawa: Murtala Zhang