Darajar naira ta daga, ta koma N470 a kan dala 1 a kasuwar ‘yan canji


DAGA IRO MAMMAN
 
Darajar naira ta karu a cikin wannan makon bayan ta samu mako biyu cikin karaya idan an canza ta da dala a kasuwar ‘yan canji.

A ranar Laraba ta samu karin N20, ta koma N470 a kan dala 1.

Kafin wannan lokaci, naira ta karye da N30 a kan dala, domin canjin ta a kasuwa ya tashi sosai zuwa N500 a kan dala 1 daga ranar Litinin, 30 ga Nuwamba zuwa N470 a dala 1 a ranar Juma’a, 20 ga Nuwamba, 2020.

To amma sababbin ka’idojin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fito da su a ranar Litinin, 30 ga Nuwamba, wadanda su ka ba mazauna kasar waje damar cin moriyar biyan kudi ko tura kudi a asusun su na cikin gida, damar su karbi kudin su a kudin ƙasashen waje, shi ya dakatar da faduwar darajar da naira ke yi.

A sakamakon haka, sai naira ta samu karin N10 a kan dala 1 a ranar 1 ga Disamba a yayin da canji a kasuwa ya fadi zuwa N490 a kan dala daga N500 kan dala a ranar Litinin.

Hakan ya ci gaba da faruwa har zuwa safiyar Laraba, amma da babban kari, domin canji a kasuwa ya kara faduwa zuwa N470 a kan dala daga N490 a kan dala a ranar Talata, wanda ya nuna an samu karin N20 a kan dala. Saboda haka dai, naira ta juyo da karfin ta inda ta kifar da faduwar N30 da ta yi a kan dala tun daga ranar 20 ga Nuwamba, 2020.

A cewar Shugaban kungiyar ‘yan canji ta Nijeriya (ABCON), Alhaji Aminu Gwadabe, ya ce wannan karin daraja da naira ta samu ya nuna dacewar sabuwar dokar da bankin CBN ya kawo wajen karbar kudaden da mazauna kasar waje ke biya.

Ya ce: “Ba shakka, ya kamata duk masu boye kudin kasar waje su fito su sayar a yanzu, idan ba haka ba za su kwan ciki.”

Yayin da ya ke karin bayani kan yadda sabuwar dokar za ta shafi samuwar dala da kuma hadahadar kasuwar ‘yan canji, Gwadabe ya ce, “An karya mamayar da (bankuna) su ka yi kuma wannan dokar za ta kawo yawaitar kudi a kasuwar ‘yan canji.

“Da gaske ne cewa yawan kudin da ake biya daga kasar waje a lokacin da ake hutun korona har yanzu su na da yawan gaske. Hasali ma dai, sauran kasashe kamar Kenya da Zimbabwe sun fi mu samun kudaden da mazauna kasashen waje ke shigowa da su saboda kwararrun likitocin da ke akwai a kasashen waje.

“Ana sa ran Nijeriya za ta rufe shekarar nan da sama da $20 biliyan daga kudin da mazauna waje ke kawowa duk da annobar korona da aka shafa da ita a cikin 2020.

“Wanda zai ci moriya ya na da ‘yancin karbar kudin sa a takardar kudin kasar waje kuma ya zuba su a bangaren kasuwar ‘yan canji, wato BDC, wanda hakan zai haifar da daidaiton farashi a kasuwar.”