Darussan da ya kamata Nijeriya ta koya daga ƙasashen Vietnam da Malaysia – Adesina

Daga AMINA YUSUF ALI

Wani rahoto ya bayyana cewa, Vietnam ta samu nasarar fitar da miliyoyin mutanen ƙasar daga cikin qangin talauci a shekaru 30 da suka wuce ta hanyar fitar da kayayyakinta zuwa ƙasashen waje, inji Akinwumi Adesina, shugaban Bankin Cigaban Afirka.

Kasuwancin ƙasar Vietnam ya kama Dalar Amurka biliyan 380 a shekarar 2020. Don haka a cewar sa, ya kamata Nijeriya ta yi koyi da ƙasashen Asiya. Domin Najeriya jimillar kasuwancinta na ƙasar waje ya kama Dala biliyan 33.5 a shekarar 2020.

Wato kaso 10 cikin ɗari na Vietnam. Sannan su kuma Najeriya kasuwancinta ya dogara kacokan da man fetur ne. Inji shi.

Adesina ya ƙara da cewa, jimillar kasuwancin ƙasar waje na ƙasar Malaysia a shekarar 2020 ya kama Dalar Amurka biliyan 234. A lokacin da kiɗan kasuwancin wajen ya fara sauyawa, sai ƙasar ta Malaysia ta samo wasu hanyoyi na sauya rawar don samun nasara. Kuma daga ƙarshe kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Adesina ya ƙara da cewa, abin mamaki ne a ce har yanzu Nijeriya ta kanta take yi a matsayinta na ƙasa mafi samar da mai a Afirka.

Abinda ya jawo haka kuwa a cewar sa, ta kasa maye gurbin man fetur da wasu kayan da za ta iya fitarwa zuwa ƙasashen wajen duniya. A cewar sa, wannan rashin tsari ne ya jawo.

Kuma a cewar sa, Abubuwan da Nijeriya take shigo da su ƙasar mafi yawansu na’urori ne da ake ƙera su a Vietnam da Malaysia. Kuma su ƙasashen suke fitarwa su kawo mata.

Ita kuma Nijeriya takan fitar da ɗanyen man fetur zalla, sannan ta shigo da tataccen mai daga wajen ƙasar, a cewar sa.

Sannan ya ƙara da cewa, Nijeriya tana cigaban tafiyar hawainiya kuma za ta iya yin abinda ya fi haka. Ya kamata a farka daga bacci a samar da hanya mai ɓullewa. A cewar sa.

Haka a cewar sa, akwai wahalar gudanar da masana’antu matuqa a Nijeriya, abinda ya sa wasu kamfanoni da dama guduwa wasu ƙasashen da za su iya gudanar da masana’antunsu cikin sauƙi.

A kan haka yake ganin dole Najeriya ta tashi daga ɗawainiya da talauci zuwa masu ɗawainiya da dukiya, ya kamata a cewar sa a ce talauci tuni ya zama tarihi a ƙasar Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *