Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), a ranar Asabar, 23 ga watan Nuwamba, ta sake tabbatar da ƙin amincewa da sabon ƙudirin gyaran haraji.
NEF ta bayyana shi a matsayin manufar “gallaza wa al’umma”, ta ƙara da cewa yana barazana ga haɗin kan ƙasa.
Kungiyar ta soki yadda aka aiwatar da ta, inda ta yi zargin cewa an mayar da masu ruwa da tsaki ciki har da mambobin Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) a gefe yayin aiwatar da ƙudurin.
Shugaban ƙungiyar ta NEF, Farfesa Ango Abdullahi, a wata sanarwa bayan taron kwamitin amintattu na biyu, a Abuja, ya yi gargaɗi kan manufofin da ka iya ƙara mayar da albarkatun arewa saniyar ware.
Kungiyar ta yaba wa ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa da kuma majalisar sarakunan arewacin Nijeriya da suka nuna adawa da ƙudurin, inda suka kira matsayinsu na kishin kasa, tare da yin kira ga ‘yan siyasar Arewa a majalisar dokokin ƙasar da su tofa albarkacin bakinsu.
Ya ce: “Taron ya tabbatar da cewa, a halin da ake ciki yanzu, dokar sake fasalin haraji an yi ta ne cikin rashin imani, ba a shirya shi ba, kuma barazana ce ga hadin kanmu da haɗin kan ƙasa.