Dattijon ƙasa, Musan Musawa ya rasu yana da shekara 86

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa dattijon ƙasa, Alhaji Musan Musawa rasuwa yana da shekara 86.

Marigayin ya rasu ne ranar Talata bayan fama da rashin lafiya.

An haifi marigayin ne ran 1 ga Afrilun 1937, tsohon ɗan jarida, diflomasiyya, siyasa ne.

Ya rasu ya bar ‘ya’ya da dangi da dama, ciki har da mataimakiyar kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC, Barista Hannatu Musawa, wadda marubuciya ce a Jaridar Leadership.

Tuni zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhini tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin.

Cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata, Tinubu ya bayyna marigayin a matsayin ɗaya daga cikin mazajajen da suka sha gwagwarmaya wajen nema wa Nijeriya ‘yancin kai.

Kana ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya saka shi a Aljanna, sannan ya bai wa iyalansa haƙuri da juriyar wannan rashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *