DCP Abba Kyari ya ƙi aminta da abincin kurkuku ya dogara ga girkin matarsa

Daga BASHIR ISAH

Babban jami’in ɗan sandan nan da ake ci gaba da tsare shi a gidan yari, wato DCP Abba Kyari, ya nuna shi ba zai ci abincin gidan yari ba sai dai abincin da matarsa ko ‘yan’uwansa suka girka.

A zaman shari’a na ƙarshe da aka yi, kotu ta ƙi yarda da batun bada belin Abba Kyari tare da wasu jami’ai huɗu da ake tuhumarsu tare.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta maka Abba Kyari tare da wasu mutum huɗu a Babbar Kotun Abuja ne bisa tuhumarsu da hannu cikin harƙallar hodar ibilis mai nauyin 17.55kg.

Bayan kammala zaman shari’a na baya-bayan nan ne alƙalin kotun, Justice Emeka Nwike, ya bada umarnin a ci gaba da tsare Kyari a gidan yari tun da ba a cimma buƙatar bada belinsa ba.

Majiyoyi daga gidan yarin da ake tsare da Kyari sun ce, tun da Kyari ya shiga gidan yarin ya ƙi cin abincin gidan, sai dai abincin da matarsa ko ‘yan uwansa suka girka suka kawo masa.

Haka nan, bayanai sun nuna cewa fursunonin da Kyari ya cim musu a kurkukun sun ji daɗin ganin sa a tsakaninsu kasancewar shi da rundunarsa ta IRT su ne suka gudanar da binciken da ya yi sanadin zuwan wasunsu kurkuku.

Wani jami’in kula da gidan yarin ya ce, “Da ma mun yi zargi mai yiwuwa ba zai ci abincin da ake bayarwa a nan ba. Saboda haka, ganin abincin da matarsa ko ahalinsa kaɗai suka girka ya buƙata hakan bai zo mana da mamaki ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *