Delta: Haɗarin mota ya ci jarirai 2 da wasu mutum 4

Daga FATUHU MUSTAPHA

Wani mummunan haɗari da ya auku a jihar Delta, ya ci ran jarirai biyu da na wasu mutum huɗu.

Haɗarin ya auku ne a ranar Alhamis a kan babbar hanyar Asaba zuwa Ughelli cikin ƙaramar hukumar Oshimili ta Arewa.

Bayanai sun nuna haɗarin ya auku ne a sakamakon aikin gyaran hanyar da ke gudana a yankin wanda hakan ya tilasta abubuwan hawa yin amfani da gefe ɗaya na hanyar.

Sai dai wasu da abin ya faru a gabansu, sun ce gangacin direbobin da haɗarin ya rutsa da su na daga cikin dalilin da suka haifar da aukuwar haɗarin.

Wani ganau ya faɗi cewa, “Mutum shida sun mutu nan take, ciki har da jarirai guda biyu, sannan kimanin wasu mutum shida sun ji rauni.”

Ya zuwa haɗa wannan labari, ƙokarin da aka yi don jin ta bakin hukuma ya ci tura.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*