Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya bada kuɗaɗe da kayan masarufi da suka haɗa da shinkafa ga iyalan jami’an tsaro na al’umma (community watch corps) da ‘yan banga waɗanda ‘yan bindiga suka kashe a ƙananan hukumomin Faskari da Sabuwa.
Haka suma iyalan mutanen da ‘yan bindiga suka kashe a garuruwan da ke ƙananan hukumomin su ma sun sami tallafawa daga gwamna Raɗɗa.
Garuruwan kuwa sun haɗa da Mararraban Mai Horas, Unguwar Liman,Tashar Nawa da Samari.
Sauran sun haɗa da Unguwar malam Tukur, Unguwar malam Hussaini,Yar lagwada, Sayau,Magarori da Yar gamji.
Mataimaki na musamman kan kula da ‘yan gudun hijira Sa’idu Ibrahim Ɗanja ya faɗi haka a hira da manema labarai a Katsina.
Ya ce gwamnatin Dikko Raɗɗa za ta cigaba da tallafawa iyalan waɗanda ‘yan bindiga suka kashe ko raunana su a duk lokacin da hakan ta taso domin sauƙaƙa masu halin rayuwa.
Malam Dikko Raɗɗa ya jinjina wa jami’an tsaro da suka rasu bisa sadaukar da rayukan su wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar wanda haka ba zai tafi a banza ba,yace.
Gwamnan ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin sa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Suma da su ke tsokaci akan tallafin shugabannin ƙananan hukumomin Faskari da Sabuwa sun yabawa Dikko Raɗɗa bisa ƙoƙarin da yake yi wajen dawo da tsaro a yankunan da ‘yan ta’adda suka ɗaiɗaita.