Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Alhaji Muhammed Idris Malagi, ya bayyana cewa, dimokuraɗiyya ba ta da wani amfani muddin ba za ta haifar da cigaba da haɗin kan al’umma ba.
Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai a Ma’aikatar, Suleiman Haruna, ya ce Ministan ya bayyana haka ne yayin da mambobin jam’iyyar APC na shiyar Arewa ta Tsakiya suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja a ranar Juma’a.
“Wannan ne ma ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa batun haɗin kai da bunƙasa tattalin arziki muhimmanci ga jama’armu, ni ma wannan shi ne saƙon da nake isarwa’,” in ji shi.
Malagi ya ce akwai buƙatar ‘yan Nijeriya su zamanto masu bincikar kansu, tare da kira ga mambobin APC da a haɗa kai don ciyar da ƙasa gaba.
Ya ƙara da cewa, burin wayar da kan ‘yan ƙasa ne samar da canjin da ƙasa ke buƙata, kuma kowane ɗan ƙasa ya duba sannan ya taka rawar da ta kamata don amfanin ƙasa.
Haka nan, ya buƙaci mambobin jam’iyyar da su haɗa kan jama’a zuwa ga fahimta da yaɗa ƙudurin gwamnatin kan yadda ya kamata ƙasa ta kasance.
Yana mai cewa, za a cimma haka ne ta hanyar amfani da hanyoyin da jam’iyya ke da su.
A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa a Arewa ta Tsakiya, Alh. Bawa Rijau, a madadin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya taya Malagi murna dangane da muƙamin Minista da ya samu.