Direban motar da jirgin ƙasa ya yi awon gaba da ita a Legas, ya nemi afuwa

Daga BASHIR ISAH

Direban bas ɗin da ta yi hatsari da jirgin ƙasa ran Alhamis da ta gabata a Legas, Oluwaseun Osinbajo, ya nemi afuwar waɗanda hatsarin ya rutsa da su a cikin motar.

Direban ya yi zargin matsalar da motar ke fama da ita a wannan lokaci ya sa hakan ta faru.

Tuni dai aka tura direban, wanda ma’aikaci ne a Ma’aikatar Sufuri ta Jihar Legas, Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar don gudanar da bincike kan aukuwar hatsarin.

Motar da lamarin ya shafa ta yi taho-mu-gama da jirgin ƙasan ne ɗauke da ma’aikatan da ke ƙoƙarin zuwa wajen aiki.

Majiyarmu ta ce an ji lokacin da direban ke cewa, “Ba laifina ba ne. Ta yaya zan yi fatali da alamomin gargaɗi? Motar ce ke da matsala.

“Abin tausayi ne faruwar haka. Ina roƙon kowa ya gafarce don Allah,” in ji shi.