Daga BASHIR ISAH
Alamu masu ƙarfi na nuni da cewar akwai yiwuwar ‘yan Nijeriya su fuskanci ƙarin kuɗin wutar lantarki nan ba da daɗewa ba.
Hakan zai faru ne biyo bayan buƙatar da gamayyar kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) mai ƙunshe da kamfanoni 11 ta nuna kan ƙarin farashin lantarkin.
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ce ta bayyana haka a ranar Juma’a, 14 ga Yulin 2023.
A cewar NERC, Gwamnatin Tarayya ta ce buƙatar sake duba farashin ta taso ne kan buƙatar haɗa sauye-sauye a ma’aunin tattalin arziki da sauran abubuwan da suka shafi ingancin sabis, ayyuka da ɗorewar kamfanonin.
NERC ta ƙara da cewa, buƙatar Discos na ƙarin kuɗin wutar lantarkin ta jingina ne da Sashe na 116 (1) and 2(a&b) na Dokar Wutar Lantarki ta 2023.
Ko a farkon wannan wata na Yuli, wasu kamfanonin rarraba wutar lantarkin sun yi yunƙuri cilla farashin wutar latarkin sai dai hakan ya gamu da cikas sakamakon nuna rashin jin daɗinsu da ‘yan ƙasa suka yi.