DisCos za su yi ƙarin kuɗin wutar lantarki ya zuwa 1 ga Satumba

Hukumar Kula da Sha’anin Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta sahale wa kamfanonin rarraba wutar lantarki su 11(DisCos) damar ƙara kuɗin wutar lantarkin da ake sha daga ranar 1 ga Satumba 2021.

Bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna cewa, hukumar NERC ta bai wa kamfanonin damar cajin kuɗin wuta gwargwadon yadda suke bada ita ne cikin wasiƙar da ta fitar mai taken “Sanarwar Ƙarin Kuɗin Wuta”.

Binciken MANHAJA ya gano cewa, tuni kamfanin rarraba wutar lantarki na Eko Electricity Distribution Company (EKEDC), ya sanar da kwastomominta a hukumance cewa zai ƙara farashin lantarki daga ranar 1 ga Satumba mai zuwa.

Kamfanin ya bayyana cewa ƙarin zai shiga cikin dokar lantarki na Oktoban 2021 wanda hakan zai kasance madadin lantarkin da za a sha na Satumban 2021.

Ya zuwa haɗa wannan labarin, duk ƙoƙarin da manema labarai suka yi don jin ta bakin mai magana da yawun kamfanin, Dr. Usman Arabi, hakan ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *