Dodanni sun kai hari coci, sun yi wa fasto dukan tsiya a Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu gungun matsafa da ake yi wa laƙabi da Dodanni, sun kai hari wani coci a Jihar Filato, inda suka tarwatsa gungun masu ibada, tare da yi wa faston dukan kawo wuqa.

Kamar yadda Jaridar Vanguard ta ruwaito, matsafan sun kai harin ne ranar Lahadi a yankin Shikal da ke Ƙaramar Hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato a daidai lokacin da mabiya ke ibada.

Maharan sun lalata kayayyakin cocin, kamar su ganguna da kayan waƙoƙi, tare da tarwatsa mabiya da suka taru suna gudanar da sujuda a cikin cocin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa matsafan sun yi dirar mikiya harabar cocin ne a daidai lokacin da mabiya suka haɗu suna gudanar da addu’a, inda suka shiga fashe-fashe da dukan duk wanda suka gani a wajen.

Jama’a sun ta gudun yada ƙanin wani domin tsira da ransu, yayin da tsautsayi ya faɗa kan faston cocin suka yi masa ɗan karen duka, kamar yadda majiyar tamu ta shaida mana.

Yankin Shikal na daga cikin wuraren da masu bautar dodanni ke da ƙarfi a Jihar Filato, sai dai a ‘yan shekarun nan Kiristoci suna yi masu ɗauki ɗaiɗai, abin da ke ta’azzara rashin fahimtar juna a tsakanin ɓangarorin biyu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Filato, Alfred Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce suna jiran cikakken bayani kafin ya bayyana abin da ya san ya faru.

Ya ce, “DPO na yankin ya tabbatar mana da faruwar wannan harin. Suna can suna aikin tattara bayanan haƙiƙanin abin da ya faru don sanin halin da ake ciki, tare da kwantar da hankali a yankin. Ya faɗa mana cewa matsafa sun kai hari cocin ne inda suka tarwatsa taron masu ibada. Ana ci gaba da gudanar da bincike. Za mu sanar da ku cikakken abin da ya faru nan gaba kaɗan.”

Wannan dai ba shi ne karon farko da matsafa ke kai hari coci ba, a baya ma sun taɓa kai hari makamancin wannan a yankin Epinmi Akoko a jihar Ondo.

A lokacin harin an kama ɗaya daga cikin matsafan, Tunde Arohunmolase, yayin da suka jikkata fastocin cocin biyu, Jacob Ogunmola da Kehinde Ilori, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.