Dogarawan Shehun Borno huɗu sun rasu a hatsarin mota

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Maiduguri

Mutum huɗu ne a cikin dogarawan Fadar Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi, suka gamu da ajalinsu sakamakon wani mummunan hatsarin motar da ya rutsa da su a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Bugu da ƙari, gawarwakin mamatan sun ƙone ƙurmus, yayin da mutum uku suka tsallake rijiya da baya, tare da raunuka a hastarin.

Wannan mummunan haɗarin ya afku ne ranar Litinin, kusa da ƙauyen Benishiek, kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, lokacin da tawagar Shehun Borno take kan hanya, sa’ilin da ɗaya daga cikin motocin ayarinsa ta yi hatsari, inda nan take ta kama da wuta.

An kwashi gawarwakin da ma waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri don yi musu magani.

Wani ganau ya bayyana cewa, “Mutum huɗu ne suka ƙone ƙurmus, uku kuma sun tsallake rijiya da baya tare da raunuka a hatsarin.”

Wani babban jami’in ‘yan sanda a Jihar Borno, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar hatsarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *