Dokar ta-ɓaci a Ribas: Dakatar da gwamna da sauran zaɓaɓɓu saɓa wa doka ne – NBA

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya, NBA, ta yi tsokaci game da hukuncin da Shugaba Bola Tinubu ya yi na sanya dokar ta-ɓaci da dakatar da gwamna da zaɓaɓɓun ƴan majalisar dokoki a Jihar Ribas.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin jawabinsa na ranar 18 ga watan Maris, inda ya ce ya yi hakan ne don kawo ƙarshen rikicin siyasar jihar.

Saidai, a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta, Mazi Afam Osigwe (SAN), NBA ta ce hakan ya yi nesa da biyayya ga doka da tasiri ga tafiyar da harkokin demokraɗiyya musamman idan an yi la’akari da sashe na 305 na kundin dokar ƙasa na 1999, wanda ke magana akan hukuncin sanya dokar ta-ɓaci.

Ya ce, duk da cewa sashen ya amince wa shugaban ƙasa sanya dokar, to kuma ya shar’anta wasu ƙa’idodi domin tabbatar da cewa ba a saɓa wa shugabancin demokraɗiyya da ƴancin ɗan-adam ba.

NBA ta koka kan yadda Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Udo da zaɓaɓɓun ƴan Majalisar Dokokin jihar na tsawon watanni shida, inda ta ce kundin na 1999 bai bai wa Shugaban Ƙasa damar cire zaɓaɓɓen gwamna ko mataimakinsa ko mambobin majalisar dokoki ba a yayin sanya dokar ta-ɓaci. Saidai, sashe na 188 ya zayyano hanyoyin da za a bi wajen yin hakan a ƙarƙashin dokar da kuma dokokin zaɓe, ya na mai cewa ba a bi ko ɗaya daga cikin su ba.

Haka kuma, ƙungiyar ta ce sanya dokar ta-ɓaci bai nuna rushewa ko dakatar da zaɓaɓɓiyar gwamanti ba – dokar ƙasa ba ta bai wa shugaban ƙasa ikon cirewa ko maye gurbin zaɓaɓɓun jami’ai ba.

Ta ƙara da cewa, sashen da ke bada damar sanya dokar ta-ɓaci ya zayyano sharuɗɗa kamar haka; yaƙi, fargabar yaƙi, tashin-tashina da ya zama barazana ga zaman lafiyar al’umma, ɓarkewar wata annoba a jiha ko wani sashinta da wasu ƙalubale da ka iya zama barazana ga ƙasa, inda ta ke ƙalubalantar ko Ribas ta kai wannan matakin.

Har’ilayau, NBA ta ce idan rikici ne na siyasa, ana amfani ne da shari’a da hukunce-hukuncen da dokar ƙasa ta bayar, ba matakin shugabancin ƙasa ba.

Ta bayyana hakan a matsayin abinda aka yi ba bisa doka ba da kuma zama haɗari ga ci-gaban shugabancin demokraɗiyya.

Don haka ne ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta Tarayyar da ta yi watsi da hukuncin shugaban ƙasar da kuma dukkan masu-ruwa-da-tsaki wajen sanya ido a shugabancin jihar don ƙaurace wa saɓa wa doka da rashin mutunta mulki a jihar.