Dokar zaɓe: Buhari ya ƙi amincewa da Sashe na 84

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna rashin amincewarsa da sashe na 84 (12) na dokar zaɓe da ya sanya wa hannu a ranar Juma’a yana mai cewa sashen ya hana wa masu riƙe da muƙaman siyasa damarsu.

Buhari ya ce Dokar Zaɓen 2022 da aka yi wa kwaskwarima tana ƙunshe da alƙaura da dama na burin inganta sha’anin zaɓen ƙasar nan da kuma gabatar da sabon tsarin amfani da fasahar zamani.

Yayin bikin sanya wa dokar hannu a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, Buhari ya shaida wa Majalisar Ƙasa da ta hanzarta gyara Sashe na 84 (12) su cire shi, wanda a cewarsa sashen ya haramta wa masu riƙe da muƙaman siyasa su yi zaɓe ko a zaɓe su yayin tarurrukan jam’iyyu.

Kafin wannan lokaci an ta cece-kuce kan ƙin sanya wa dokar hannu da Buhari ya yi a baya, sai ga shi a dokar ta samu shiga a wannan karon.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila da sauransu na daga cikin waɗanda suka hallarci bikin sanya wa dokar hannu.