Dokar zaɓen Buhari da ta INEC

Ta tabbata dai shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan amincewa da dokokin zaɓe kuma kwana kaɗan sai ga wani jadawali na hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta sanya ranaku da lokuttan zaɓe mai zuwa na 2023.

Hakan duk wani cigaba ne kuma ko shakka ba bu waccen doka ta zaɓe daga ɓangaren zartarwa da ita kanta hukumar zaɓen alamu ne waɗanda ke nuna zahiri an ɗauki hanyar gyara wacce talakka zai yi zaɓe bisa zaɓin shi.

Amma har haka adalci ne mai gyara duk wata doka musamman ta zamantakewa domin duk wata doka da mutane za su zauna su tsara ba lalle ba ne ta zamo gamsassa ga kowa musamman yadda siyasa ke canja ababe da fatan Allah yai ma mu jagora a lamurammu, Amin.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. 07066434519, 08080140820.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *