Dole a kamo waɗanda suka kashe kwamishinan Jihar Katsina, inji Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da rahoton kashe kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina, Dakta Rabe Nasir da aka yi a yammacin ranar Alhamis.

Shugaban a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a yammacin ranar Alhamis, ya bayyana kisan kwamishinan a matsayin wani mummunan aiki da Allah wadai da shi, inda ya ƙara da cewa, “ba zai yiwu a riƙa samun irin wannan tashin hankali a ƙasarmu ba.”

Shugaban ya ce, ya ji takaicin kisan gillar da aka yi wa wannan shugaba mai tasowa wanda ya yi wa al’ummarsa da jiharsa da ƙasa baki ɗaya hidima da ƙwazonsa.

“Tunanina yana tare da dangin mamacin,” inji shugaban.

Ya buƙaci jami’an tsaro da su yi cikakken bincike tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu wajen aikata laifin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *