Dole a kawo ƙarshen cin zarafin ’ya’ya mata a Nijeriya – Ƙungiyar SOHI

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar ‘Save Our Heritage Initiative’ (SOHI), wata ƙungiya mai zaman a Abuja, ta sake yin kira da a kawo ƙarshen duk wani nau’i na cin zarafin mata da ake yi.

Shugabar ƙungiyar, May Ikokwu, ta yi wannan kiran ne a wata hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya, a yayin bikin ranar mata ta duniya (IWD) 2022 a Abuja ranar Talatar da ta gabata.

Rahoton ya ce, Majalisar Ɗinkin Duniya ta kafa ranar 8 ga Maris a matsayin ranar mata ta duniya domin wayar da kan al’umma kan al’amuran da suka shafi mata da ’yan mata tare da samar da hanyoyin magance su.

Gangamin na amsa kiran ‘#BreaktheBias’ a matsayin taken sa na shekara.

Ikokwu, wadda ta taya mata a faɗin duniya murnar wannan rana, ta kuma tunatar da su kan buƙatar yin amfani da wannan dama wajen wayar da kan mata da maza, musamman mata masu tasowa.

Ta ce, “cin zarafi ga mata babban cin zarafi ne na haqqin ɗan adam. Haka zalika hakan na shafar matsayin aure.”

“Ta dogara ne a kan tsattsauran ra’ayi, zubar da ra’ayi, ɗabi’un zamantakewa da ke jurewa da kuma amincewa da munanan ayyukan tashin hankali kamar hana samun damar mallakar dukiyar miji da dai sauran su,” inji ta.

Ta kuma nanata bukatar mata su san haƙƙinsu na gado a kan dukiyar iyali da filaye.

A ci gaba da haka, ta buƙaci sarakunan gargajiya da su tabbatar da kare haƙƙin mata a yankunansu. Mai kare rajin kare haƙƙin ta kuma bayyana cewa, mace za ta iya zama duk abin da ta ke so a rayuwa.

Ikokwu, wadda ta bayyana rashin basu haƙƙinsu a wurin kulawa a matsayin wani nau’i na cin zarafin mata, ta yi kira da a ƙara haɗa kai daga mata da masu ruwa da tsaki domin kawo ƙarshen wannan barazana.

Ta ƙara da cewa, “hana ’yancin cin gashin kai a fannin kulawa yana nuni da yanayin da wasu mutane ke yanke wa mata hukuncin da ba sa so.”

Sai dai kuma ta yi kira ga mata da su yi amfani da wannan rana mai albarka wajen wayar da kan tsofaffin mata game da haƙƙinsu, da ƙarfafa musu gwiwa wajen samun ayyukan tallafi, da haɗa kai da ƙungiyoyin farar hula domin haɗa kan al’umma don kawo ƙarshen wannan annoba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *