Dole ne Japan ta daina goyon bayan masu ra’ayin nuna ƙarfin soja

Daga CMG HAUSA

Ranar 15 ga watan Agustan bana, aka cika shekaru 77 da ƙasar Japan ta sanar da mika wuya ba tare da gindaya sharaɗi ba, amma al’ummomin ƙasashen duniya suna damuwa matuka, saboda sun ga yunƙurin da wasu ‘yan siyasar ƙasar masu ra’ayin nuna ƙarfin soja suke nunawa, musamman ma kan batun Taiwan.

A kwanakin baya bayan nan, shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta sabawa manufar “ƙasar Sin ɗaya kacal a duniya”, ta kai wa yankin Taiwan na ƙasar Sin ziyara, inda ta sha suka daga ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da kasa sama da 170.

Amma firayin ministan Japan Fumio Kishida ya bayyana yayin da yake ganawa da Pelosy cewa, matakan soja da kasar Sin ta ɗauka a kusa da tsibirin Taiwan sun kawo ƙalubale ga tsaron ƙasar Japan. Ya kara da cewa, Japan da Amurka za su kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan tare.

Haƙiƙa Japan ba ta da haƙƙin yin sharhi kan batun Taiwan ko kaɗan.

Sojojin Japan sun taba kai wa tsibirin Taiwan hari, har da kwace tsibirin da sauran kananan tsibirai a yankin a shekarar 1895, inda Japan ɗin ta yi mulkin mallaka har na tsawon shekaru hamsin, tare kuma da hallaka mazauna yankin Taiwan sama da dubu 600, lamarin da ya jefa Taiwan cikin mawuyacin yanayi mai tsanani.

Kana bayan Japan ta mika wuya a yaƙin duniya na biyu, kasar Amurka ba ta hukunta masu ra’ayin nuna ƙarfin soja na Japan ba, bisa la’akari da moriyarta, lamarin da ya sa har yanzu masu ra’ayin nuna karfin soja na Japan ke ci gaba da kokarin gudanar da mulkin mallaka a yankin Taiwan.

Kowa ya sani, bai kamata ‘yan siyasar Japan su manta da masifun da suka kawo wa sauran ƙasashen Asiya maƙwabtansu ba, ya dace su yi la’akari da darasin tarihi, kuma dole ne su daina goyon bayan masu ra’ayin nuna ƙarfin soja.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa