Don ƙwato wa mata ‘yanci na zama lauya – Amina Ladan Abubakar

“Sarautar Magajiya Babba dama ce ta cikar burina”

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Idan a na maganar masu hidimta wa jama’a, to Hajiya Amina Ladan Abubakar ta shiga sahun matan, saboda gudunmawar da ta bayar ga cigaban mata ta fannoni da dama. Da yake alkhairi ba ya tafiya a banza, in da ka yi shi sai ka samu sakamakon sa. Don haka ba abin mamaki ba ne Hajiya Amina Ladan Abubakar ta samu sakamako na girmamawa, saboda Alkhairin da ta shuka. A kwanakin da suka gabata ne dai Mai Martaba Sarkin Tsibirin Gobir da ke Jamhuriyar Nijar ya duba dacewarta da nasabarta da gidan Sarautar Tsibirin Gobir, ya naɗa ta a matsayin ‘Magajiya Babba’ a masarautarsa, wadda kuma sarauta ce da a ke bai wa ‘ya’yan sarki a masarautar. Wakilinmu a Kano, ya tattauna da ita, don haka sai ku biyo mu, ku ji yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatunmu.
Hajiya AMINA: To alhamdu lillahi. Ni dai farko, sunana Hajiya Amina Ladan Abubakar, wadda a yanzu zan iya cewa na samu ƙarin suna da sarautar ‘Magajiya Babba’ Tsiburin Gobir, wadda Mai Girma S. M. Alhaji Abdul Balla Marafa, Sultan na Gobir ya naɗa. kuma Tarihin rayuwata; Ni dai haifaffiyar garin Kano ce, a cikin Ƙaramar Hukumar Nassarawa, kuma a nan Kano na yi karatu, daga baya aka yi min aure na zauna a garin Jega da ke Jihar Kebbi, zuwa yanzu Ina da yara guda huɗu.

Ta ɓangaen fafutukar rayuwa kuma fa?
Alhamdulillahi. A rayuwa duk wanda ya samu tarbiyya a gidansu, to za ka ga duk in da yake za ka ga yana gudanar da rayuwa da zamantakewa da jama’a mai kyau. Don haka ni ka ga ban tashi a garin Jega ba, aure ne ya kaini, amma na ji da]in zamantakewa ta a garin Jega, kasancewar kyakyawar mu’amala da na ke da ita da mutane, kamar dangin miji da sauran abokan mu’amala ta yau da kullum. Wannan ta sa har na zama wata jigo a garin da a yanzu idan ka ambaci suna na duk a garin lallai za a ce an sanni, duba da shahara irin ta gidan su mijina, kasancewar gidan ‘yan boko ne, kuma ‘yan siyasa, masu nagarta.

To, a ‘yan kwanakin da suka wuce, kin samu kan ki a matsayin mai riƙe da sarautar Magajiya Babba ta Tsibirin Gobir. Ko za ki bayyana wa masu karatunmu yadda kika samu wannan sarautar da kuma yadda ta samo asali?
E to, kamar yadda na faɗa ma ka, mu gidanmu mun taso daga babban waje, sannan kuma mahaifinmu mutum ne da ya yi mu’amala da mutane manya sosai, na nan Kano da kuma sauran jihohin Sakkwato da Kebbi, to, mu na da kyakyawar alaƙa da sarauta kamar yadda mu ke jin tarihi a wajen ‘yan’uwan mahaifinmu, su na faɗa ma na nagartar zuri’arsu da sarauta. To ikon Allah da yake mu na da ɗan’uwa da Allah ya ɗaga darajarsa, wato Aminu Ala, wanda ya shahara ya yi suna a duniya, to sai ya zama ta silar wanna ɗaukaka da Allah ya yi masa, sai ta zama jagora na zuwa nemo asalin mahaifanmu, don haka ne har mu ka samu kan mu a matsayin ‘yan asalin Sarautar Tsibirin Gobir ta tsatson kakanmu, don haka da aka bai wa Aminu Ala, ni ma sai ya jawo ni, saboda kusancinmu da sarautar, don haka sai na samu kaina a matsayin sarauniyar a cikin sarautar, wadda aka ba ni matsayi mai girma, wanda yake na ‘ya’yan sarki, don haka na zama ‘ya a cikin Masarautar Gobir, na zama Magajiyar Girma da a ke kira Magajiya Babba Tsiburin Gobir, wadda zan iya wakiltar ‘ya’ya mata game da matsalolinsu na rayuwa, zan iya zama wakiliya a tsakanin mu mata a kan sha’ani na rayuwar yau da kullum.

To wannan sarauta ta ki, sai a ke ganin wani aiki ne ba na wasa ba. Ko ya za ki tunkari gudanar da ita?
Ai kamar yadda na ke faɗa ma ka, ita ɗaukaka wata abu ce daga Allah, yadda Allah ya taimake mu, ɗaukakarmu da nasabarmu ta kaimu har zuwa wannan waje aka yi mana wannan naɗi, a fili cikin jama’a, kuma mutanen gari suka karɓe mu hannu biyu, kuma suka yarda lallai mu na gidan ne, ba taka haye mu ka yi ba, haka kuma yadda wajen bai yi mana nisa da zuwa ba domin karɓo wannan sarauta ta gidanmu, to haka ba za mu gajiya ba a kan hidimar da ta taso za mu yi, iya iyawar mu, domin ganin ita masarautar da kuma garin za mu je mu gudanar da abin da ya kamata mu bayar da gudunmawarmu da taimakonmu kamar yadda mu ka yi alƙawari.

Ko ya kika samu kan ki a lokacin da aka naɗa ki wannan sarautar?
Kai! Na ji daɗi sosai, don gaskiya in ban da Ubangiji Allah shi ne ya ke ɗaga darajar bawan sa ai ban san zan kai ga samun wannan matsayin ba, don haka na ji daɗi kuma na yi godiya ga Allah, don yadda mu ke murna a ranar da ni da ‘yan’uwana, abin alfahari ne da mu ka gano mu na da kyakyawan tsatso da asili mai nagarta, kuma a shahararriyar masarauta. A wannan yankin na Afirka, kusan babu kamarta, domin ta na da ɗumbin tarihi wanda a yanzu idan aka ba ka labarin sarkin da yake kai shi ne sarki na 380, lallai za a gane cewa, masarauta ce da ta shahara ta bunƙasa, kuma ta kasance tsohuwar masarauta mai tsawon tarihi, don haka na ji daɗi kuma Ina alfahari da Allah ya sa na fito a wannan tsatso.

To wanne buri kika sa a gaba domin gudanar da al’amuran ki na rayuwa don ci gaban jama’a?
Ina da buri sosai, domin tun kafin na san kaina cewar ina da alaƙa da wannan masana’anta, tun a baya na yi karatu na Lauya, kuma daman na yi karatun ne domin na taimaka wa ‘yan’uwana ta wajen gazawar su da ƙwato mu su ‘yanci, to ka ga wannan matsayin da aka ba ni na zama Magajiyar mata don haka na ji daɗi, saboda na ƙara samun dama ta cikar buri na da na ke ganin na zama jagorar da zan iya samun damar da zan taimaka wa mata a duk in da su ke, musamman a yanki na na Tsibirin Gobir.

Daga ƙarshe, wanne saƙo ki ke da shi?
Eh to, saƙo na dai shi ne, Ina godiya ga Allah da ya ɗaukaka nasabar mu da darajar gidanmu, ya ƙara ɗaukaka matsayin yayana Aminu Ladan Abubakar wadda shaharar sa ta sa ya samu ƙauna da soyayya a manyan masarautu na Jihar Kano da Jigawa, suka yi masa naɗi na sarauta wanda ta silar wannan abu a yanzu ga shi ya samu kan sa a ɗan sarki mai cikakken iko da daraja da nasaba ta zuri’a mai daɗaɗɗen tarihi, wanda a yanzu duk duniya ba ma shakkar mu fito mu bayyana kan mu cikin jin daɗi da kuma alfahari. Don haka mu zuri’ar Alhaji Ladan abin alfahari a gare mu.
kuma Ina matuƙar godiya ga masoya, ‘yan’uwa, abokan arziki, dangi na nesa da na kusa, da waɗanda suka taka rawar gani wajen zuwa su raka mu karɓar wannan sarauta har zuwa fadar mai Martaba Sarkin Gobir, kuma muna godiya ga waɗanda suka raka mu da addu’a. Sannan Ina babbar godiya ga Sultan Abdu Balla Marafa da wannan naɗi da ya yi mana. Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana cikin aminci da nagarta.

To madalla, mun gode.
Ni ma na gode sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *