Don bai wa matsa aiki gwamnati ta ƙirƙiro aikin gina layin dogo a sassan ƙasa – Amaech

Daga UMAR M.GOMBE

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya ce babbar manufar Shugaba Muhammadu Buhari na gina layin dogo a sassan ƙasa ita ce don samar da aikin yi ga matasan Nijeriya.

A Lahadin da ta gabata Minista Amaechi ya bayyana haka ta hannun hadimarsa kan sha’anin yaɗa labarai, Mrs Taiye Elebiyo-Edeni, yana mai cewa ayyukan samar da hanyoyin jirgin ƙasa da ke kan gudana za su taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce, bayan kammala layin dogo da ake ginawa a gabashin ƙasa hakan zai zama silar samar da gurbin aiki tsakanin 20,000 zuwa 50,000 baya ga sauran harkokin kasuwanci da za su buɗu.

Ya ƙara da cewa, ayyukan samar da hanyar jirgin ƙasar da suka fi muhimmanci su ne; na Lagos zuwa Kano da na Fatakwal zuwa Maiduguri saboda ɗimbin kayayyakin da za a riƙa jigilarsu a hanyoyin bayan kammalawa.

Amaechi ya ce burin Ma’aikatar Sufuri shi ne tabbatar da kammala ayyukan da za su taimakawa wajen bunƙasa fannin tattalin arzikin ƙasa.