DSS ta buƙaci ‘yan jarida da su tabbatar da ingancin labari kafin wallafawa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta DSS, Kwamanda Hassan I. Muhammad ya buƙaci ‘yan jarida da su haɗa kai da hukumar wajen samar da tsaro da haɗin kai da zaman lafiya a Nijeriya.

Daraktan ya yi wannan kiran ne yayin da yke karɓar baƙuncin shuganni da mambobin ƙungiyar ‘yan jarida masu yaɗa labarai a shafukan sadarwa na zamani wato Association of Kano Online Jounalist a ranar Laraba da ta gabata.

Hassan I Muhammad ya ce kafar yaɗa labarai ta internet kafa ce mai sauƙi, da ake yaɗa labaran ƙarya da ke haddasa ruɗani da tarzoma a cikin al’umma.

Ya ƙara da cewa samuwar ƙungiyar ‘yan jarida masu gudanar da ayyukan su a shafukan intanet ba na kokonto zai taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaron da gwamnatin ƙasar nan ke ci gaba da yaƙi da su.

”Dama dai mun daɗe muna jiran irin wannan lokaci da za a samar da wata inuwa da za ta haɗa kawunan ‘yan jarida wajen gudanar da ayyukan da ya kamata.

”Ta hanyar wannan ƙungiya na san za ku iya bayar da gudunmawa wajen samar da sahihan labarai kuma ingantattu ga jama’a,” inji Hassan I. Muhammad.

A nasa ɓangaren muƙaddashin shugaban ƙungiyar Malam Yakubu Salisu, ya ce sun kai ziyarar ne domin gabatar da ƙungiyar ga hukumar ta DSS domin yin aiki kafaɗa da kafaɗa wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban al’ummar jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Yakubu Salisu ya ce maƙasudin kafa ƙungiyar shi ne tsaftace harkar yaɗa labarai a shafukan intanet tare da yaƙi da labaran ƙarya da kuma kalaman ɓatanci.

Jaridar Blueprint Manhaja na daga cikin ‘yan jaridar da suka kai ziyarar, inda ta ruwaito cewa Daraktan Hassan I. Muhammad ya ja hankalin mambobin ƙungiyar da su zamo masu bin doka da oda a lokacin da suke gudanar da ayyukansu tare da sanya kishin qasa domin samun zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.