Hukumar tsato ta DSS ta tsare Manajan Jirgin ƙasan a Abuja-Kaduna na Kaduna, Pascal Nnorli, biyo bayan takardar sanarwar gargaɗin yiwuwa kai wa jirgin hari da ta bayyana.
Majiya mai tushe daga Hukumar Jirgin Ƙasa ta Nijeriya ta shaida wa jaridar News Point Nigeria an tsare Manajan ne tare da Manajan Ayyuka na hukumar, Victor Adamu da kuma wasu ma’aikatan hukumar.
Blueprint Manhaja ta rawaito a makon jiya DSS ta yi gargaɗin tsaro ga hukumar inda ta ce ta bankaɗo shirin ‘yan bindiga na yiwuwar kai harin kan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna kowane lokaci.
Cikin sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan DSS na shiyyar Abuja, R.N. Adepemu, hukumar ta gargaɗi fasinjojin da ke mu’amala da jirgin da su yi hattara.
Majiyar News Point Nigeria ta ce, “Kun san cewa tun ranar Alhamis da ta gabata aka tsare Manajanmu? Su biyu aka tsare amma an sako ɗayansu.”
“Yanayi ne kawai ya ritsa da Victor saboda cim masa da aka yi a ofishin Pascal, don haka aka haɗa da shi da sauran ma’aikatan Pascal aka kwashe su zuwa ofishin DSS. Har yanzu Pascal na can,” in ji majiyar.
Da aka nemi jin ta bakinsa kan batun, Majan Darakta na NRC, Fidet Okhiria, ko uffan bai ce ba.