Daga BASHIR ISAH
Hukumar tsaro ta DSS ta yi zargin cewar akwai wasu da ke ƙoƙarin haddasa fitina don wargaza zaman lafiya a faɗin ƙasa.
Da wannan DSS ta hanzarta gargaɗin masu hannu cikin wannan mummunan ƙuduri da su janye ƙudurin nasu ko kuma su fuskanci fushin dokokin Nijeriya.
Gargaɗin na DSS na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ta fitar ta ofishin Jami’in Yaɗa Labarai na DSS, Dr Peter Afunanya.
A cewar sanarwar, “Hukumar na gargaɗin waɗanda suka zaƙu don tada zaune tsaye a ƙasa da su janye aniyarsu.
“Ya isa shaida ganin yadda wasu fusatattun ‘yan siyasa da suke ganin an yi musu ba daidai ba suka fara amfani da haramtacciyar dama.
“Duk da dai dimokuraɗiyya ta gaji haka, sai dai kuma DSS ba za ta naɗe hannu sannan ta zuba ido tana kallon ana yi wa zaman lafiyar ƙasa barazana ba,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa, masu ingiza mutane zuwa ga kalaman ɓatanci da labaran ƙarya game da gwamnati mai jiran gado a dukkanin matakai, da su daina.
Ta ce babu wata riba da masu neman tayar da zaune tsaye za su samu in ban da salwantar da kansu da ma waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.
Kazalika, Hukumar ta ce abin damuwa ne matuƙa yadda wasu fitattun ‘yan ƙasa ke amfani da kafafensu wajen ɓatar da jama’a wanda a cewarta, hakan ba daidai ne ba.