Daga BASHIR ISAH
Jami’an DSS sun dake tsare dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, bayan rikita-rikuta da jami’an kula da gidan gyaran hali.
Manjaha ta tattaro cewar an sake tsare Emefiele ne jim kadan bayan da Babbar Kotun Tarayya a Legas ƙarƙashin jagorancin Alƙali Nicholas Oweibo ta ba da belinsa kan Naira miliyan 20.
Yayin zaman Kotun a ranar Talata Alƙali Oweibo ya ba da umarnin a tsare Emefiele a kurkuku har sai ya cika sharuɗɗan belin da aka gindaya masa.
Jim kaɗan bayan hukuncin ne sai jami’an DSS suka shirya kansu a wajen kotun inda suka sake tsare Emefiele bayan kuma DSS sun tara ‘yan kallo tsakaninsu jami’an gidanyari.