DSS ta shigar da ƙarar tuhumar ta’addanci akan Mahdi Shehu

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sandan farin kaya ta DSS ta shigar ƙarar tuhume-tuhume guda biyar da suke da alaƙa da ta’addanci akan ɗan gwagwarmayar kai, Mahdi Shehu, a Babbar Kotun Tarayya dake Kaduna.

A kwanan nan ne DSS ta kama shi sakamakon yaɗa wani bidiyo acikin al’umma, wanda a ciki ake bayanin cewa Gwamnatin Nijeriya ta bai wa ƙasar Faransa damar kafa sansanin sojoji a Arewa.

Da farko dai DSS ta maka ɗan gwagwarmayar ne a kotun inda ta buƙaci a tsare shi na kwanaki 60 bisa tuhumar sa da laifukan da suka shafi ta’addanci.

A lokacin da ya ke gabatar da sauraron ƙarar, Mai Shari’a Rilwan Aikawa, ya umarci DSS da ta tsare Shehu na tsawon kwanaki sittin don bai wa jami’an hukumar damar kammala bincike akan sa.

Blueprint ta ruwaito cewa ana tuhumar Mahdi Shehu ne da abubuwa kamar haka: yaɗa bayanai na ƙarya don haddasa tashin-tashina; yaɗa bayanan ƙarya da suke da alaƙa da ta’addanci; gangancin yaɗa labarin ƙarya; da zargin ƙarya akan cin amanar ƙasa; da kuma amfani da soshiyal mediya don samun goyon bayan zarge-zarge mara asali da suke barazana ga ƙasa.

Waɗannan laifuka ne da suka saɓa wa dokar ƙasa a ƙarƙarshin manyan laifuka da na yanar gizo.