Dubai: Mutum 422 aka ɗauki nauyinsu zuwa taron COP-28 – Malagi

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta maida martani kan ce-ce-ku-cen da ke yi game da adadin mutanen da ta ɗauki nauyi zuwa babba taron COP-28 da ke gudana a Dubai.

Rahotanni sun ce tawagar Nijeriya na ɗaya daga cikin tawagogin da suka fi yawan mambobi da suka halarci taron wadda ke ƙunshe da mutum sama da 1000.

Sai dai a ƙarin hasken da ya yi game da wannan batu, Ministan Labarai da Wayar da da Kan ‘Yan Ƙasa, Mohammed Idris Malagi, ya ce, “Mutum 422 ne Gwamnatin Tarayya ta ɗauki nauyinsu zuwa wurin taron”, amma ba sama da 1000 kamar yadda aka yayata ba.

Idris ya yi cikakken bayani a cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin inda ya ce daga cikin waɗanda aka ɗauki nauyinsu zuwa wajen taron sun haɗa da jami’ai da hukumomi da ma’aikatun gwamnati.

Ya ce, an ɗauki nauyin mutum 32 daga Hukumar Kula da Sauyin Yanayi, 34 daga Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, ma’aikatu 167, da mutum 67 daga Fadar Shugaban Ƙasa.

Sai kuma mutum 9 daga Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, 40 daga Majalisar Tarayya da kuma cikibiyo da hukumomi 73.