Dubai ta soke harajin sayar da barasa domin jan hankalin baƙi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumomin Dubai sun soke harajin da ake biya na kashi 30 cikin 100 na sayen barasa a wani yunƙurin zawarcin ’yan yawon buɗe ido.

Jama’a za su daina biyan kuɗin harajin da suke bayarwa na ƙa’ida na samun izinin barasa a gida, wanda sai sun yi haka ne suke da damar sha ba tare da cewa sun keta doka ba.

A baya-bayan nan Dubai na ta sassauta dokokinta inda take bayar da damar sayar da barasa a fili kuma a rana tsaka hatta a cikin watan azumi na Ramadan, tare kuma da amincewa da kai barasar gidaje ga mabuƙata a lokacin annobar Korona.

Ana ganin duka waɗannan matakan da hukumomin ke ɗauka wani ƙoƙari ne na jan ‘yan ƙasashen waje birnin domin gogayyar da suke fuskanta daga makwabtan ƙasashe.

Kamfanoni biyu da ke hada-hadar barasa a birnin na Dubai, Maritime and Mercantile International (MMI), da kuma African & Eastern, sun ce za su rage farashin barasar sakamakon cire musu harajin da aka yi.

Kakakin kamfanin MMI, ya yaba da matakin, inda ya sheda wa Kamfanin Dillancin Labarai na AP, cewa, “Tun da muka fara harkokinmu a Dubai sama da shekara 100 da ta gabata, matakan da masarautar ke ɗauka abin a yaba ne domin tana la’akari da zamani tare da ƙoƙarin tafiya da kowa.”

Ya ce, “Waɗannan sauye-sauye da aka yi a kan dokokin za su tabbatar da masu buƙata na saye da shan barasar hankali kwance ba tare da wata fargaba ba a Dubai da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan gaba ɗaya.”

Sai dai ya ce, ba su sani ba ko matakin hukumar da ya fara aiki ranar Lahadi zai kasance na dindindin.

Jaridar Financial Times ta bayyana matakin da cewa na gwaji ne na shekara ɗaya, inda ta alaƙanta majiyarta da manyan jami’an harkokin kasuwanci.

Ma’aikata ’yan ƙasashen waje sun ninka ‘yan ƙasa tara a Dubai, kuma mazauna birnin da ke shan barasa yawanci suna tafiya Umm al-Quwain da sauran birane domin sayen barasa mai yawa idan suna buƙata.

Da man shi birnin Dubai yana samun ‘yan yawon buɗe idanu da attajiran ma’aikata ‘yan waje fiye da makwabtansa, galibi saboda sassaucin dokokinsa.

To, amma a yanzu birnin na fuskantar gogayya daga wasu daga cikin maƙwabtan ƙasashe da birane, inda suma suka tashi domin bunƙasa harkokinsu na yawon buɗe idanu da vangare samun kuɗaɗensu.

Duk wanda ba Musulmi ba ne da ke zaune a Dubai dole ya kasance ya kai shekara aƙalla 21, kafin ya sha barasa ko ya yi safararta ko ya ajiye ta a gida, sannan kuma dole ne ya kasance ya samu takardar izinin hakan, wanda wani kati ne na musamman na roba da ’yan sanda ke yarjewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *