Dujiman Katsina ya musanta zargin ƙaurace wa mazaɓarsa

Hon. Aliyu Abdullahi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majalisar Wakilai, Hon. Aliyu Abdullahi, kuma Dujiman Katsina, ya musanta zargin da Abdullahi Musawa ya yi masa na ƙaurace wa mazabarsa.

Abdullahi Musawa ya yi zargin ne a wata kafar sadarwa ta yanar gizo inda ya soki ɗan majalisar da ƙaurace wa mazaɓarsa duk da matsalar tsaro da yankunan ke fama da shi.

Saidai mataimaki na musamman kan yaɗa labarai, Mr Francis Sardauna a wata takarda da ya fitar, ya musanta batun zargin da Abdullahi Musawa ya yi wanda ya yi hakan ne don neman ɓata wa Dujima suna saboda buƙatar kansa.

“Ganin yadda ɗan majalisar ke samar wa al’ummar mazaɓarsa
abubuwan more rayuwa yasa shi Abdullahi Musawa ya nuna hassada da rashin samun nitsuwa saboda tsananin adawa”, inji Francis.

Ya kuma ce Hon. Aliyu Abdullahi mai wakiltar Musawa da Matazu da aka zaɓe shi a ƙarƙashin jam’iyar APC ba zai taba ƙaurace wa mutanensa da su suka zaɓe shi ba.

“Ko a kwanan nan ya kai ziyarar ta’aziya a ƙauyukan Ruwan Ƙusa da Ƴar Unguwa da Gidan Malamai a Musawa da Matazu inda ya tallafa masu da miliyoyin nairori.”

Haka kuma Dujiman ya tallafa wa matasa da kuɗi Naira miliyan 35 domin inganta sana’o’insu da tallafa wa naƙasassu da keken hawa mai ƙafa uku guda 100.

“Hatta shi Abdullahi Musawa da yake zargin ɗan majalisar, kwanan ya ba shi gudummawar N900,000 da zai aurar da diyyarsa”, inji Francis.

Har’ilayau, Dujiman ya samar wa matasa da dama aiki, ya gina makarantu da masallatai da bunƙasa sana’o’i a mazaɓarsa.

Kazalika, ya ce wannan zargi ba zai hana shi cigaba da kawo wa mutanensa abubuwan more rayuwa da inganta rayukansu ba.