
Daga BELLO A. BABAJI
Kamfanin MTN ya ƙara farashin kira zuwa N13.8 a kowane minti daga N7.8.
Wani bincike ya nuna cewa an yi wani kira na daƙiƙu 62 aka, lamarin da ya nuna an samun ƙarin farashi da kaso 43.
Hakan ya biyo bayan haƙuri da kamfanin ya bayar na ƙara kashi 200 ne ga kuɗin datar giga 15.
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, MTN ya ce an samu kuskure a lissafin gyaran farashin, inda ya tabbatar wa kwastomomi cewa yana ƙoƙarin ganin an samu sabis mai kyau a nan gaba.