Duk da bambancin addinin da ke tsakanina da matata, littattafanmu ba su faɗa da juna – Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya babbaya wa duniya wani abun da kan wakana a tsakaninsa da matarsa, Oluremi Tinubu.

A cewar ɗan siyasar, matarsa da ta kansance mai bin addinin Kirista shi kuma Musulmi, kan ajiye littafin Baibul ɗinta a kusa da Ƙur’aninsa ba tare da samun wata mishkila ba.

Tinubu ya bayyana haka ne a wani shafinsa na soshiyal midiya, inda ya ce duka litattafan biyu masu tsarki kan kasance ajiye wuri guda alhali ba a samun wata rashin jituwa a tsakaninsu.

A cewarsa, “A ɗakin kwananmu, matata kan ajiye littafin Baibul ɗinta a gefen Ƙur’anina, kuma wani abu guda ɗaya da na fahimta shi ne, littattafan biyu kan kasance tare wuri guda ba tare da wani saɓani ba.”

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake tirka-tirkar wanda zai yi wa Tinubu mataimaki a takarar shugabancin ƙasa da yake yi a ƙarƙashin APC ya zuwa zaɓen 2023.

Yayin da Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta nuna rashin amincewarta da musulmi biyu su yi takarar shugaban ƙasa da mataimaki, wasu masu ruwa da tsaki sun buƙaci ‘yan Nijeriya da su maida hankali wajen duba cancantar ɗan takara a maimkon akasin hakan.

Wasu sun yi hasashen cewa, waɗannan kalamai na Tinubu sun nuna yadda yake riƙo da addini da kuma dattako kan sha’anin addini.

Kawo yanzu dai shugabannin APC a Arewa maso Yamma sun matsa lamba wajen ganin kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa ta koma yankinsu

Rahotanni sun nuna cewa, shugabannin APC na yankin sun gudanar da wani taro a ranar 30 ga Yuni, 2022, taron da ya samu halarcin gwamnonin APC da ‘yan takarar gwamna har da ministoci.

An ce jagororin sun yanke matsaya kan cewa za su tafi su gana da Tinubu don gabatar masa da baƙarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *