Duk da dokar taɓaci kan ilimi a Sakkwato, firamare ta Ruggar Giwa na cikin wani hali

Daga AMINU ALHUSSAIN AMANAWA a Sakkwato

Makarantar firamaren Ruggar Giwa dai na a ƙauyen Tuntube ne dake yamma da garin Shuni na ƙaramar hukumar mulkin Dange-shuni dake jihar Sakkwato, tafiyar aƙalla mintuna 15 zuwa 20 daga ƙauyen zuwa ƙwaryar birnin Sakkwato.

Makarantar wacce aka kafa sama da shekaru 40 da suka gabata, na cigaba da kasancewa cikin halin ka’ka’ni kayi, na lalacewar ajijuwa, da ofishin shugaban makaranta, da ma na malamai, uwa uba rashin kayan rubutu da na karatu da makarantar firamaren ke fama da shi.

A cewar ɗaya daga mazauni ƙauyen Malam Muhammad Naira Tuntube, yanayin da makarantar ke ciki na jefa tunanin su cikin halin ni’yasu.

“Mukan kasance cikin bakin ciki a duk lokacin da muka dubi tsan-tsar halin da wannnan makarantae ke ciki da yaran mu ke karatu, wacce aka kafa tun a shekarar 1970, duk da yake cewa bamu da matsalar malamai a wannan makarantar, amma halin da makarantar ke ciki abun damuwa ne matuƙa.”

Shi ma da yake magantawa shugaban ƙungiyar iyayen yara da malamai na makarantar da ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da kwamitin da yake jagoranta ke yi, lamarin da makarantar ke ciki na son gagarar kundila.

“A matsayin mu na kwamitin iyayen yara da ɗalibai na wannan makarantar, muna ƙoƙari na ganin iyaye sun tura yara makaranta, duk kuwa da halin da makarantar ke ciki, amma duk da haka anamu ɓangaren muna ƙoƙari wajen samar da runfuna duk dai domin tabbatar da cewa yaran mu sun samu ingataccen ilimi da za su zamo masu amfani ga al’umma nan gaba kaɗan.”

Duk da lalacewar da makarantar tayi a yanzu makarantar ƙauyen na da sama da ɗalibai 100 da suke karɓar darussa a ƙasa da sa’oi 3 zuwa 4 a cewar ɗaya daga cikin ɗaliban makarantar.

“Muna karantar da yara ne na sa’oi 3 zuwa huɗu a rana, watau daga ƙarfe 8n zuwa 12 na rana, saboda a wannan lokacin rana za ta soma zafi, abinda yake da matuƙar wahala ga yaran su iya samun damar ɗaukar darussa kan abinda ake koya masu, don haka ne nake kira ga masu ruwa da tsaki don Allah su duba halin da wannan makarantar ke ciki su kawo mana ɗauki.”

A cewar da dama daga waɗanda wakilin namu ya zanta da su, sun bayyana rashin jin daɗin su, kan halin da makarantar tasu ke ciki, duk kuwa da cewa suna bada tasu gudunmawa wajen jefa ƙuri’u da kan kai shuwagabanni kan madafun iko.

Koda yake wannan makarantar na cikin wani hali, amma hakan bai hanawa yaran dake karatu a ciki ba, fatan zamowa wani abu nan gaba a rayuwa.

Makarantar Firamare Ruggar Giwa

“Sunana Hafsat ɗaliba a wannan makarantar ta Ruggar Giwa ina da burin son zama abubuwa da dama a rayuwa nan gaba, amma halin da makarantar mu ke ciki na sanya ni damuwa, kan ko burin nawa zai iya cika.”

Da halin da makarantar ke ciki dai a yanzu hakimin ƙauyen ya yi kira da babbar murya na a kawo masu ɗauki domin magance masu abubuwan da suke buƙata, da zai bawa malamai damar gudanar da ayukkan su, yadda ya kamata.

Sai dai lokacin da aka tuntuɓe sa daraktan wayar da kan jama’a na hukumar bayar da ilimi bai ɗaya ta jihar Sakkwato Dr. Kabiru Aliyu, ya bayyana cewa sam ba sa sane da halin da makarantar ke ciki, amma da samun wannan labarin za su yi duk mai yuwa wajen magance wannan matsalar.

Ya ƙara da cewa “kuma ina bai wa al’ummar ƙauyen Ruggar Giwa ta ƙaramar hukumar mulkin Dange shuni  cewa, bada ɓata lokaci ba za mu yi wani huɓɓasa akai.”

Idan dai za a iya tunawa a shekarar 2015 Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ayyana dokar ɗaukin gaggawa a bangaren ilimin jihar Sakkwato.