Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna, KAEDCO, ya buƙaci mutane da su biya kuɗin wuta duk da tsawon lokacin da aka ɗauka babu wutar lantarki a Arewa.
Jaridar Manhaja ta ruwaito cewa an samu katsewar wutar lantarki a Kaduna, Katsina, Kano da Jigawa sakamakon lalacewar turakun lantarki a layin 330KV na Shiroro zuwa Kaduna da kuma matsalar layin Ugwuaji zuwa Makurɗi.
Wannan lalacewar ya bar jihohin da abin ya shafa cikin duhu na tsawon kwanaki.
Amma cikin wata sanarwa da babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Abdulazeez Abdullahi, ya fitar, kamfanin ya buƙaci abokan cinikin sa da su biya kuɗin sabis din da aka samar kafin katsewar wutar lantarkin.
Yayin da yake tabbatar da irin wahalar da mazauna jihohin da abin ya shafa suke fuskanta, sanarwar ta ce, “Mun fahimci cewa ya kasance kwanaki masu wahala a ‘yan kwanakin nan saboda katsewar wuta da ba a yi tsammaninsa ba. Muna tunatar da cewa katsewar ta fara ne a ranar 20 ga Oktoba. Muna kuma sake ba da haƙuri.
Duk da haka, abokan ciniki su sani cewa dole ne su biya kuɗin wutar lantarkin da aka yi amfani da ita daga ranar 1 ga Oktoba zuwa ranar 19 ga Oktoba. Wannan yana nufin za a yi lissafin kwanakin da aka samar da wutar lantarki a wannan watan.
“Muna godiya da fahimtar ku da haɗin kan ku a wannan lamari. Idan kuna da wasu tambayoyi ko matsaloli, kada ku yi jinkiri don tuntuɓar sashen kula da abokan cinikin mu a cibiyar kula da abokan ciniki ko ofishin yankin ku.