Duk dillalin da ya ƙara farashin kayayyaki a bakin lasisinsa – BUA

Daga FATUHU MUSTAPHA

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu, ya yi barazanar ƙwace lasisin duk wani dillalin kamfanin da aka kama ya tsawwala farashin kayayyaki yayin watan Ramadan.

Alhaji Abdulsamad Rabiu ya bai wa al’umma tabbacin kamfaninsa ya tanadi wadatattun kayayyakin masarufin da za su ishi ɗaukacin jihohin ƙasar nan a lokacin Ramadan da kuma bayansa da zummar hana faruwar matsin da ‘yan ƙasa kan fuskanta da zarar watan Ramadan ya kama.

Shugaban BUA ya bayyana haka ne ta bakin wakilinsa na yankin Arewa, Alhaji Mohammad Adakawa, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kano.

Adakawa wanda fitaccen ɗan kasuwa ne a kasuwar Singer da ke Kano, ya ce rukunin famfanonin BUA ya samar da wadatattun sukari da Spaghetti da filawa da sauran kayayyaki waɗanda tuni suna kasuwa da kuma jihohin faɗin ƙasar nan da nufin hana farashin kayayyaki tashin goron zabbi, musamman ma a lokutan bukukuwa.

Ya ce, “Ina tabbatar muku da cewa muna da isassun kayayyakin da za su wadaci dukkanin jihohin Arewa, mun tanadi sukari mai yawa a Sharaɗa wanda zai wadaci jama’ar Kano, Kebbi, Jigawa, Yobe, Maiduguri, zamfara da kuma Katsina baki ɗaya. Kuma BUA ya bada tabbacin ba zai ɗaga farashin kayayyakinsa ba a Ramadan da kuma bayansa.

“Galibin jama’a ba su san musabbabin tashin farashin kayayyaki ba a Ramadan, sau tari kamfanoni ne ke haddasa tsadar kayayyaki daga tushe. Amma da wannan mataki da BUA ya ɗauka, ina da yaƙinin bana ba za a yi fama da tsadar kyayyakin masarufi ba”.

Daga nan, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakin rage haraji ga ‘yan kasuwa masu shigo da kaya domin samun sassaucin shigo da kayayyaki cikin ƙasa.