Duk inda aka san ni in har zan shiga zan samu karramawa fiye da hamshaƙan mutane – Ɗan Sarauta

Ɗan Sarauta

Ibrahim Adam wanda yawancin mutane su ka fi sani da Ɗan sarauta, ya kasance wani baharu a fagen rubutacciyar waƙa da kuma waƙoƙin zamani na Hausa. A zantawar sa da jaridar Manhaja ya kwararo bayanin yadda ya tsinci kansa a fagen waƙa da rubuce-rubucen zube da sauran su. Sannan ya faɗi irin ƙalubalen da marubuta waƙa ke fuskanta. Ga dai yadda hirar ta kasance, domin an ce waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi.

Daga AISHA ASAS a Abuja

Mu fara da jin tarihin ka.
Suna na Ibrahim Adam, amma an fi sani na da Ɗan Sarauta. An haife ni a shekarar 1992 a unguwar gidan waya da ke cikin birnin katsina. Na yi karatun Muhammadiyya a makarantun Musulunci, sannan daga bisani na shiga ɓangaren karatun zamani wato (Boko). Na fara karatu a matakin firamare a makarantar ‘Maƙera Primary Katsina’, daga shekarar 2001 zuwa 2007, na yi ƙaramar sakandire a makarantar koyar da Larabci da ilimin Musulunci, da kuma horon malamai, wato ‘Sir Usman Nagogo College of Arabic and Islamic Studies’ (SUNCAIS) a shekarar 2008 zuwa 2011. Bayan na gama qaramar sakandire sai na tafi Government College Katsina inda na kammala karatu na na babbar sakandire a shekarar 2014. Daga nan sai na tafi makarantar koyar da ilimin kimiyya ta katsina wato Hassan Usman Katsina Polytechnic (HUK) inda na karanta ‘office technology and management’ (OTM), tare da makarantar horon lauyoyi da ke garin Daura, Dr. Yusuf Bala Usman ‘College of Legal and General Studies’ Daura (CLGS) nan kuma na yi karatu a ɓangaren Harshen Larabci da Musulunci, wato ‘Arabic and Islamic Studies’. Haka zalika ban yi ƙasa a guiwa ba, na yi karatu a ɓangaren na’ura mai qwaqwalawa wato a makarantar Umaru Musa ‘Yar-adu’a ‘Capacity and Capability Development Center’.
Bayan nan kuma na je makarantar ‘Eva-green Schoolarship and Skills Aquisition Business Seminars’, inda nan ma na yi karatu a ɓangaren aiki da na’ura mai ƙwaƙwalwa. A gaskiya na yi karatuttuka da dama, a gurare daban-daban. Sannan kuma ina koyarwa a Islamiyyu inda har ta kai ina mallakar shedar koyarwa ta makarantun boko da islamiyyu. Yanzu haka ina neman ilimi a kowane fanni, m’ana Arabi da Boko. Inda kuma na ke bisa ga koyar da karatu a makarantun Islamiyyu da sauran gurare, wannan shi ne tarihi na.

Shin wane irin mawaƙi ne kai?
Ma sha Allah, ni mawaƙin zamani ne, amma wani lokacin na kan tsinci kai na a layin mawaƙan gargajiya. Wanda na kasance na kan yi waƙoƙi kala daban-daban, kama daga waƙar biki ko suna, jinjina, siyasa, talla, da dai sauran su. Haka zalika na kan yi waƙoƙin zube irin na mutanen baya, wanda na ke karantawa a gurin tarurruka musamman tarurrukan marubuta.

Wace shekara ka fara waƙa?
Na fara waƙa a shekarar 2014, inda na fara da waqa ta ‘Happy sallah’.

Shin ka na rubuta waƙoƙin ka da kanka ne, ko wani ke rubuta ma ka?
A gaskiya ni ne na ke rubuta waƙoƙina da kaina. Kuma tunda na ke babu wanda ya taɓa rubuta min waƙa na rera. Duk wata waja da za a ji na yi, to ni ne na ke rubutawa. Kuma har ma na kan rubuta ma wasu kamar yadda aka san cewa akwai wanda su ba sa rubuta waƙa sai dai kawai su rera. To ni ina rubutawa ina rerawa. Kuma ina rubuta ma wasu su rera Alhamdu lillah.

A ɓangaren rubutu akwai marubutan waƙa, akwai marubutan zube da na wasan kwaikwayo, shin kai a wane rukuni ka ke, ko a wane fanni ka fi ƙwarewa?
Eh to, lallai kamar yadda na faɗa a baya cewa, ni marubucin waƙa ne, to amma kuma duk da haka ina yin rubutun zube, wanda shi kan shi rubutun zuben, na ɗan yi nisa a ciki duk da cewa ni kallon da na ke wa kaina ban zamo komai ba face mai kishin rubutu da marubuta.
Amma wasu masu bibiyar rubutun na wa har sun fara karrama ni da lambar yabo, a matsayin fasihin marubucin da ya ke tasowa, wannan kam na san nasara ce daga Allah shi ya sa na ke ƙara gode masa a kowane lokaci, Alhamdu lillah.
Haka kuma, na kan yi rubutun wasan kwaikwayo, duk da cewa shi ban daɗe ina rubutawa ba, amma dai bakin gwargwado shi ma na fara fahimtar sa, kuma idan na yi ana yabawa.
Gaskiya na fi ƙwarewa a rubutun waƙa, duk da shi rubutun waƙa ya na buƙatar salo, saita amo, da kuma ƙafiya. To ni duk wannan ba sa tada min hankali ina jin daɗin rubutun waƙa.

Menene ya ba ka sha’awa har ya sa ka tsunduma harkar waƙa?
Babban abinda ya ba ni sha’awa a harkar waƙa wanda har ya sa na tsunduma cikin yin waƙar shi ne, isar da saƙo cikin sauƙi, sannan kuma saƙon da aka isar a waƙa ya kan yi tasiri ga mutane sosai fiye da yadda za a saka lasifika ana sanar da mutane saƙon.
Bayan na fara waƙa a matsayin ina son aikawa al’umma saƙonni, to a cikin karatuttukan da na ke yi sai na tsinci cewa ashe har al’ummar Larabawa da su ka daɗe a duniya ta hanyoyi biyu su ke aika saƙo, kuma sun ɗauki wannan hanyoyin ne don su na da tabbacin su na isar da saƙon cikin sauƙi kuma cikin sauri.

Hanya ta farko ita ce waƙa, hanya ta biyu ita ce huɗuba, misalin irin wacce ake yi ranar juma’a idan an haɗu don gabatar da sallar juma’a.

To amma ita wannan hanyar ba ta kai waccan ta farkon tasiri ba, saboda ita daga sati sai sati, ita kuma waccan a kullum ne, shi ya sa su kan su Larabawa su ka fi raja’a da yin waqa a matsayin hanyar isar da saƙo.

Ka na da malami ne ko wani ubangida wanda za ka nuna a matsayin wanda ya koya ma ka waƙa?
Gaskiya ba ni da malami ko ubangida a harkar waƙa, domin ni ban san lokacin da na koya ba, kawai dai na ji ina yin waƙa wanda idan na zauna ni kaɗai sai abubuwa su riƙa faɗo min daga nan sai in kama nazari.

Wannan ne ya ba ni ƙwarin guiwa har na tsaya na rubuta waƙa ta farko mai suna ‘Happy Sallah’, daga nan sai na tafi ‘studio’ na rera, amma babu wanda ya koya min waƙa. Saboda haka gaskiya ba ni da ubangida ko malami a harkar waƙa. Asali ma ni ba ni da wata alaƙa da mawaƙa har sai da na fara waƙa sannan na san mawaƙa, na ji ni kawai da son haddace waƙoƙin mutane wanda ni ma daga bisani na ji ina yin nawa.

Wane irin ƙalubale ka ke ganin marubutan waƙa ke fuskanta?
Babban ƙalubale da marubutan waƙa su ke fuskanta shi ne, da yawa a cikin wanda ake rubuta ma waƙa ba kowa ya ke girmama baiwar da Allah ya yi wa marubutan ba. Wani zai zo ya haɗa ka da Allah ka rubuta masa waƙa ya rera, amma ya na jin zafi ya ce kai ne ka rubutu masa, wani lokacin shi ne zai fara kushen ka cikin mutane. Wannan shi ne babban ƙalubalen marubutan waƙa.

Ana kiran ka da Ɗan sarauta, shin wannan wata sarauta ce ko kuwa ya abin ya ke?
Eh, yanzu kam akwai sarautar gama sunan ta (Wadatan matasan Hausa) duk da cewa ahalin mu su na da sarauta to wannan suna nawa ba can ya nufa ba. An ƙirƙiri wannan suna a bisa wata ɗabi’a tawa wacce na kasance ba na son hayaniya, wasu lokuta idan na zo cikin mutane ana surutu sai na koma gefe, daga nan ne sai irin abokai su ce, yau fa Ibrahim sarauta ya ke ji, wannan shi ne asalin sunan Ɗan sarauta, amma yanzu kuma ni ne ‘Wadatan matasan Hausa’,, ina ƙarƙashin sarkin matasan Hausa.

Shin ku na da wata kungiya ce ta mawaƙa wadda ku ke tafiyar da al’amuran ku a jiha ko ƙasa bakiɗaya?
Eh mu na da ƙungiya mai suna ‘Waƙa babbar hikima’, amma iya aikin ta a nan cikin Katsina ne, sai dai ina cikin wasu wanda su ke matakin ƙasa.

Kamar yadda marubucin zube ya ke iya zubo labari nan take idan ya riƙe alƙalami, shin kai ma maganar nan da mu ke yi da kai za ka iya yi min waƙa mai ƙafiya?
Ƙwarai kuwa Aunty! Wannan abu ne mai sauƙi ki ji ina rero waqa take-yanke kuma tare da ƙafiya. Kari shi ne abin da ya fi ba ni wahala wajen ƙirƙirar waƙa. Abin da ya sa na ɗauki kari a matsayin abin da ya fi ba ni wahala wajen ƙirƙira waƙa, musamman da ga mu mawaƙan zamani a kullum ana so aji mun fito da wani sabon salo wanda ba a tava jin irin sa ba.

Duk mawaƙin zamani ya na so idan ya yi waƙa komai daɗin ta shi ke nan ya gama da ita. Misali, idan aka kawo min waƙar aure ko jinjina, ba abin birgewa ba ne in yi wa ango da amarya waƙa yau, kuma gobe in sake yin kalarta ga wasu, illa iya ka kawai sunaye ne za a canza. A’a ya na da kyau su ma ka sake sabon kari sannan kai ma su tasu waƙar. To a gaskiya wannan abu ya na wahalar da mawaƙa da yawa ba ma ni kaɗai ba. Wannan dalilin ne ya sanya idan mawaƙi ya ji wani kari ya zo masa to sai ya yi sauri ya rubuta shi ko da babu wanda zai yi wa waƙar zuwa gaba idan ta kama sai kawai ya yi ta ga wanda su ka zo masa.

Amma saɓanin waƙoƙin gargajiya, mutum ya na iya yin waƙoƙi kala goma da kari ɗaya. Misali ya yi wa duniya, zamani, ilimi, mutuwa da dai sauran su. Kuma duk da kari ɗaya, maganganun cikin ne kawai za su bambanta.

Ka na nufin ka ce ko wace waƙa sai mawaƙi ya ƙirƙiri na ta karin?
Ƙwarai da gaske. Idan har ya cika mawaƙi ba. Domin komai daɗin kari maimaita shi ba shi da daɗi ga masu saurare.

Waɗanne nasarori ka samu ta hanyar waƙa?
Na samu nasarori da dama ta dalilin waƙa, babbar nasar da na samu ita ce mutane. Kamar yadda ‘yan magana su ke cewa jama’a rahama ne to lallai ni na tabbatar da hakan. Domin yanzu ta kai kusan duk inda aka sanni in har zan shiga to zan samu karramawa fiye da yadda wasu hamshaƙan mutanen su ke samu, kuma duk a dalilin waƙa ne, gaskiya sai dai mu ce Alhamdu lillah, Allah ka ƙara mana masoya na gaskiya.

Ƙalubale akwai su?
Duk ɗan Adam ba ya rabuwa da ƙalubale, musamman wanda Allah ya bai wa keɓantacciyar baiwa irin mu mawaƙa da marubuta. Babban ƙalubale ma a wannan harka shi ne zagon ƙasa, da kuma son a ɓata wa wane suna. Musamman idan an ga ya na ƙoƙari Allah ya saka masa hannu a cikin harkokin sa. Ba duka su ke da wannan halin ba, a’a wasu ‘yan tsiraru ne, su ke da wannan mummunar ɗabi’a, sai dai kuma ni ban kwanta ba, ina nan ina ta yin addu’a Allah ya raba mu da sharrin masharranta albarkar Manzon Allah (SAW).

To wane kira ko shawara za ka ba sauran mawaƙa ‘yan uwan ka?
Ina kira ga sauran mawaƙa da su yarda waƙa sana’a ce kamar yadda na ga wasu sun ɗauki abin wasa da nishaɗi, sannan kuma a haɗa kai don ganin haƙa ta cim ma ruwa. Allah ya ƙara sanya mana albarka a cikin harkokin mu na rayuwa.

Ita fa gwamnati akwai rawan da za taka wajen tallafa wa mawaƙa?
Gwamnati ita ce ta ke da muhimmiyar rawar takawa idan ta janyo mawaƙa a kusa da ita. Domin kuwa yanzu mun zo wani lokaci wanda ita kanta gwamnatin ba a sanin manufofi da aiyukan ta sai ta hanyar waqa da mawaƙa. Don haka ya na da kyau gwamnati ta sanya mawaƙa cikin gwamnati tsundum, sannan kuma ta yi musu kujeru na musamman don su kare martabar ta da kuma isar da saƙon al’umma zuwa ga gwamnatin akan abin da su ke nema na alfanun rayuwa.

Ya alakar ka da sauran mawaƙa?
Akwai kyakyawar alaƙa sosai tsakani na da sauran mawaƙa, ina son su ina son cigaban su, kamar yadda su ma su ke muradin su ga na take tsani.

To maddallah mun gode
Ni ma na gode Aunty Asas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *