Duk inda Bagobiri ya ke ɗan uwana ne, inji Alan waƙa

*Aminu Ala ya ƙara samun sarauta a Masarautar Tsibirin Gobir

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Aminu Ladan Abubakar Ala, Sarkin Waƙar Masarautar Dutse, Ɗan amar Bichi, Dujiman Ƙaraye, Ɗan Buran na Sabon Birnin Gobir, mawaƙi ne da ya shahara a fagen waƙoƙin zamani wanda samun irin sa abu ne mai wahala saboda ɗaukakar da Allah ya yi masa a cikin mawaƙan zamanin.

Domin kuwa Shaharar sa ta kai shi ga samun matsayi a fadojin sarakuna da suka ba shi sarautu kamar yadda yake a sama. Kuma wannan wata ɗaukaka ce da baiwar da ba kowa yake samun ta ba a duk wani fanni na rayuwa sai ‘yan kaɗan daga cikin mutane.

A yanzu ma dai likkafar tasa a fagen rayuwa ta ƙaru, sakamakon wata sarauta mafi girma da ya samu a wannan lokacin, kuma a Masarautar Tsiburin Gobir da ke cikin Jamhuriyar Nijar wadda Sultan na Tsibirin Gobir S. M. Elh. Abdou Balla Marafa ya naɗa masa rawanin Sarkin Ɗiyan Gobir.

A ranar 13 ga Fabrairu, 2022, ne dai aka yi bikin naɗin sarautar a Masarautar Tsibirin Gobir wanda dubun dubatar mutane daga Nijeriya da kuma Nijar suka halarci wajen naɗin wanda aka yi bukukuwa na al’adar ƙasar Tsibirin Gobir da hawan Daba, sannan kuma mawaƙan da suka halarci wajen daga Nijeriya da kuma Nijar suka baje kolin waƙoƙin su. 

Manyar mutane da suka halarci wajen taro.sun haɗa da, Gwamnan Maraɗi, sai Ministoci na Jamhuriyar Nijar da sarakuna na ƙasar Gobir irin Madawa Ƙwanni, sai Kuma tawagar mawaƙa da ‘yan fim na Kannywwod da sauran su. 

Bayan taron mun tattauna da Sarkin Ɗiyan Gobir, Alhaji (Dakta) Aminu Ladan Abubakar Ala, a kan naɗin sarautar da aka yi masa musamman Nijar in da ya fara da cewar:

“To Ina godiya ga Allah da ya ba ni wannan dama kuma na san ba iyawa ta ba ce, kuma ina godiya ga dukkan sarakunan da suka ba mu aro na wata shigifa ta wakilci a cikin hurumin su na sarauta.

Ni dai kamar yadda aka sani haifaffen Nijeriya ne, kuma ɗan cikin garin Kano. Mahaifina haifaffen garin Jega ne wadda take a Jihar Kebbi, sannan wanda ya haifi mahaifina ma a nan Jega aka haife shi, saboda haka ni mutumin Nijeriya ne, mahaifina ɗan Nijeriya ne har ma da kakana. Amma kuma yau aka wayi gari ga ni da sarautar ‘ya’ya a ƙasar Gobir, Gobir ɗin kuma a cikin Tsibiri wadda take a Nijar. Amma dai wanda ya san tarihi wannan ba zai zama wani abu sabo ba, domin kuwa duk wanda zai bada tarihin kakannin sa guda biyar to sai ya ba mu labarin ta in da ya shigo Nijeriya.

Shi ya sa za ka ga tarihin masarautu zuwan Fulani wato Shehu Ɗan Fodiyo su ne suka assasa wannan Daula ta Fulani daga mutane wanda Torankawa a ke Kiran su, sun zo ne daga Toro ta ƙasar Mali. Shi ya sa ko Sarkin Zazzau na yanzu za ka ga an yi masa inkiya da Bamalle a na nufin ƙasar Mali. Saboda haka Gobirawa a daɗaɗɗen tarihin yadda suka shigo ƙasar Hausa, tun daga Magrib waɗanda suka zauna a yankin Sahara har suka shigo cikin Nijeriya ta yanzu suka zauna a wani gari da a ke Kira Alƙalawa suka kafa Daular Gobir wadda ita ce ta farko da ta yi fice a duniya tun zamanin su Bawa Jangwarzo, kuma masarautar ta yi zamani mai tsayi a tarihi.

Domin Gobirawa su ne su ke da sarakuna sama da 380 a yanzu haka a lissafi, saboda haka yaƙi ne ya sa Fulani suka matsa da su in da su ke a Tsiburi a yau, kuma suka kasu, wasu suna Nijeriya wasu kuma a Nijar. Kowa ya sani ƙasar Hausa a Nijeriya ta haɗa da yankin yamma da kuma wasu sassa na Nijar, saboda haka ne za ka samu Badauri yana da ‘yan’uwa a Nijar, kuma yana da su a Nijeriya. Haka ma Kanuri mutanen Borno suna da’ yan’uwa a Difa wadda take cikin Nijar. Ko mutanen Maraɗi, za ka ji ana Sarkin Katsinar Maraɗi, to haka sabon Birnin Gobir a Sokoto yake ga kuma Tsibirin Gobir a Nijar. To wannan ƙasar Hausa Kenan, saboda haka wannan na san ba zai bai wa masana tarihi da ilimi wahala ba.

Alan Waƙa

Saboda haka ni ɗan Sarautar Gobir ne, amma ita Gobir ba gari ba ne ƙabila ce ana yi wa Gobirawa laƙabi da ƙabilar su ba kamar Kanawa ko Sakkwatawa ko Zazzagawa da a ke yi mu su inkiya da garin su ba. Saboda haka duk in da Bagobiri yake to ɗan’uwana ne, amma dai in da masarautar mu take a yanzu ta na Tsibiri a yanzu haka, to ni kuma sai na samu kaina a matsayin ɗan sarautar garin da aka bi salsalar tarihi kamar yadda na faɗa waƙar ‘Shahara’.

Saboda haka Ina ƙara godiya ga Allah da wannan karamcin da waƙa ta nemo mini `yanci kuma ta tabbatar da ni a wata babbar sarauta ta huɗu a Masarautar Tsibirin Gobir.

Mu mu na da sarautar yaya guda sha takwas, kuma dukkansu ba a bai wa wanda ba ɗan sarautar ba sai wanda ya kasance ɗan sarki ne. Sannan ta farkon su ita ce ɗan Galadima, sai Bunu, sai Marafa, sai kuma Sarkin ɗiyan Gobir.

To Ina yi wa Allah godiya da ya yi mini wannan baiwa, kuma Ina godiya ga dukkan mutanen da suka halarci wannan muhimmin taro. Allah ya saka da alkhairi da fatan kowa ya koma gidansa lafiya.”