Duk inda ka tafi bayan miƙa mulki zan binciko ka – Tinub ga Buhari

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya shaida wa Shugaba Buhari cewar, ko da Buharin ya zaɓi zama a Daura ko ƙasar Nijar bayan rantsarwa, zai binciko shi.

Tinubu ya faɗi haka ne cikin raha da kuma martani ga kalaman da Buhari ya yi kwanan nan game da inda zai tafi bayan miƙa mulki.

A baya, an jiyo Buhari na cewa zai yi nesa da Abuja bayan miƙa mulki a matsayin Shugaban Ƙasa.

Buhari ya ce mahaifarsa Daura zai koma da zama bayan miƙa mulkin, idan ma aka matsa masa a nan Daurar, zai tsallaka ya koma ƙasar Nijar.

Ya ce Dimokuraɗiyyar Nijar nan ne gida na biyu a gare shi bayan Nijeriya, tare da cewa wannan ne ma ya sa sa’ilin da ya zama Shugaban Ƙasa ya fara kai ziyara ƙasashen Nijar da Cadi da Kamaru saboda dalilan kansa da na ƙasa.

Sai dai ra’ayin Buhari na komawa Nijar da zama ya haifar da cece-kuce a ƙasa, inda wasu ke ganin Shugaban na neman yin waskiya ne don kada ya amsa tambayoyi bayan miƙa mulki.

Wasu kuwa na ra’ayin Shugaban ya yi haka ne domin raha da kuma samar wa kansa sassaucin nauyin da yake nauke da shi.

Ya zuwa ranar Litinin, 29 ga Mayu ake sa ran Shugaba Buhari ya miƙa mulki inda kuna za a rantsar da magajinsa, Bola Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *