Duk ma’aikacin da ya bar ƙasa yana aiki dole ya dawo da albashin da aka biya shi – Tinubu

Shugaban ƙasa Tinubu yace, duk ma’aikacin da ya bar ƙasa yana aiki dole ya dawo da albashi kuma a hukunta shugaban sashensa.

Shugaban ya faɗi haka ne a yayin bikin da akai domin kammala bikin satin ma’aikata na ƙasa a Abuja continental hotel.

A yayin wannan bikin ne, shugabar ma’aikatan Najeriya ta bayyana wannan saƙon na shugaban ƙasan. Ta ƙara da cewa yanzu haka an ɗauki matakai domin shawo wannan matsalar.

Shugaban yace aikin gwamnati shine jigon kowacce gwamnati domin tafiyar da al’amuran ta. Yace don haka, ba za a bari ma’aikata su rinƙa yin abubuwa kara zube ba.