Duk macen aure na buƙatar tallafi ko mijinta na mata duk hidima – Jiddah Nguru

“Kasuwancin mata a kafafen sadarwa na ƙara masu ƙima a idon mabiyansu”

Daga AISHA ASAS 

A ci gaba da tattaunawa da matasan mata da ke da kishin kansu, waɗanda ke nema in ba kai ba ni wuri, shafin Gimbiya ya sake zaƙulo ɗaya daga cikin masu kasuwanci a kafafen sadarwa, don ta zama allon kallo ga mata irinta, kuma ta wayar da kai kan yadda mata za su iya cin moriyar intanet.

Dama dai shafin naku ne mata, don haka muke kawo abinda zai ƙara maku ƙwarin gwiwa tare da ƙarfafaku kan dogaro da kanku. Masu hikimar magana dai sun ce, duk macen da ta zauna, za ta ga zaunau.

Mai sana’ar kifi ce, dankalin turawa, manshanu da kuma gangariyar nono kindirmo, mace ce matashiya mai kamar maza, kuma mai ilimin zamani. A tattaunawar Manhaja da ita, za ku ji tarihinta da yadda ta fara, har zuwa ga ƙalubale da nasarororin da ta samu a kasuwanci a kafafen sadarwa.

Idan kun shirya, Wakiliyar Blueprint Manhaja, AISHA ASAS, ce ke tare da Jiddah Haulat Nguru: 

MANHAJA: Mu fara da jin tarihin rayuwarki.

JIDDAH NGURU: Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.
Da farko dai sunana Hauwa Shuaibu, amma wasu sun fi sanina da Jiddah Haulat Nguru. Shekaruna 33 a duniya. An haife ni a garin Nguru da ke Jihar Yobe. Anan na yi karatuna tun daga firemare har matakin gaba da sakandire. Yanzu haka Ina da aure da yara biyu, muna zaune a Jihar Kano aiki ya kawo mu. Wannan shi ne tarihina a taƙaice.

Me ki ka sa gaba a yanzu?

Abubuwa da yawa, amma mafi muhimmanci yanzu kasuwancina.

Kin kasance ɗaya daga cikin matasan mata da ke amfani da kafafen sada zumunta don neman na kai. Shin me ya sa ki ka yi wannan tunanin?

Na yi nazarin cewa, yanzu duniya ta koma kan ‘Social Media’ ne bakiɗaya. Sannan a matsayina ta mace, matashiya, matar aure, na tsaya na yi nazarin ta wacce hanya zan amfani waɗannan abubuwa, sai kawai na ga hanyar kasuwanci a gurina ita ce ta fi dacewa. Maimakon na hau na yi kalle-kalle ko na yi ta posting muna surutu, alhalin yanzu kasuwar duniya bakiɗaya ta koma ‘Social Media’, to gara na amfane ta ta wannan fannin. Na kawowa mutane abinda suke so a sauƙaƙe, ni ma na samu hanyar kuɗin shiga.

Tun da yanzu rabi da kwatan mutane bakiɗaya sun koma kan ‘Social Media’, zai yi wuya ki ga mutum ya shafe rana guda ko awa guda bai leƙo ba. To anan zai ga abinda yake so, ko wanda ma kwata-kwata babu a garinsu ya siya cikin sauƙi akai masa har gida duk yana kwance ta waya kawai za ku gama komai cikin sauƙi.

Wane alfanu mata suke samu musamman ma matan aure a kasuwanci a kafafen sada zumunta?

Alhamdulillah. Haƙiƙanin gaskiya ya sama mana alfanu musamman mu matan aure. Na ɗaya idan budurwa ce a ‘social media’ yawanci soyayya ce ta ke hawar da su zai iya yiwuwa wata shi ne alfanunta, dan har zai iya haɗa ta da mijin aure. To mu yawanci matan aure nishaɗi ke kai mu, Allah ya kiyaye idan nishaɗin ya yi yawa sai a faxa hanyar da ba ta dace ba. Amma idan kina kasuwanci yana ƙara miki daraja a gurin ‘customers’ ɗinki da mabiyanki dan sun san ba wasa ne ya kawo ki ba.

Sai abu na biyu, duk macen aure tana da buƙatar tallafin kuɗi ko da kuwa mijinta na yi mata dukkan wata hidima ta rayuwa. Kowa ya san mace da ƙyale-ƙyali da son burgewa ga rashin son raini idan bikin dangi ko ƙawaye ya zo, (dariya) ba kowa ke iyawa hidimar mace ba sai Allah. To wannan sana’ar na ƙara samar mata da hanyar biyan buqatarta cikin sauƙi ba tare da ta takurawa kowa ba.

Sannan ga hidimar yaranta. Hatta shi maigidan za a taimaka masa da abubuwa da dama, ko da kuwa ba mai son taimakon mace ba ne a gida, Dole akwai abinda za ta kare masa, akansa ko kanta ko kan ‘ya’yansa. Kin ga wannan ma ya ƙara mata mutumci da ƙima a idanunsa. Sannan zamansu zai ƙara ƙarko, Dan mazan yanzu ba sa son mace mai yawan bani-bani.

Ba mu labarin irin naki kasuwancin da yadda ki ke gudanar da shi.

Ni Ina siyar da abubuwa da ɗan dama. Na farko wanda aka fi sanina da shi shi ne, sana’ar kifi banda (dried fish) wanda kamfanin ke amfani da sunan Nguru Standard Fish Store. Sai sana’ar dankalin turawa. Yanzu sai na faɗaɗa kasuwancin kawo ingantaccen nono kindirmo na saniya , shi kuma sunansa Nguru Fresh Milk Kindirmo tare da Nguru Pure Cow Ghee Manshanu. Dukkanin waɗannan kasuwancin Ina yin su ne ta hanyar ‘Internet’, musamman Facebook, WhatsApp da Tiktok. Sannan kifi da kindirmo da manshanu daga garinmu nake sarowa na siyar.

A matsayinki ta mace ko kin haɗu da wata matsala ga irin wannan sana’a taki, kasancewar an fi danganta maza da ire-irensu?

Gaskiya ba wata matsala da na fuskanta, daga gida har waje. Alhamdulillah a dukkan kasuwancina mijina yana bani matuƙar ƙwarin gwiwa, Dan ko kaya aka kawo daga wani garin idan ba mu samu mai delivery ba , shi zai je ya ɗauko. Tare za mu kasa kayan tare za mu yi rubutu da lissafi. A zahiri ni kaɗai ake gani a kasuwancin, amma a baɗini kusan shi ne ƙarfinta.

Dan dukkan wasu wahalhalu shi yake riƙe min ragamarta. Ban da shawarwari da ƙwarin gwiwa. Ga mahaifiyata a garinmu. Duk wata zirga-zirgar nemo min kifi mai kyau da nono da manshanu ita take min. Ba ta tafiya har sai ta ga kayana sun tashi a tasha. Anan kam na qara gode wa Allah ba ni da wata matsala sai qarin ‘support’ ma da nake samu daga gurinsu a kullum.

Kin ga maganar da na yi ta sana’a yanzu wajibice akan mace ya fito. A wannan yanayin dole ne mace ta tashi ta nemi abin yi. Domin mazaje yanzu abubuwa sun musu yawa. Ga ƙarancin kuɗin ga buƙatu da hidimomin iyaye da iyalai.

Wasu matan kan ce ba za a iya haɗa taura biyu a tauna su a lokaci guda ba, na daga aiki ko sana’a da kuma kula da iyali. Ke ya ki ke haɗa biyun a tare?

Maganar gaskiya hakan ba ƙaramin aiki ba ne, akwai wahala sosai. Amma wahalarsa ba ta kai wahalar babu ba. Duk abinda ki ka ga mutum ya ce, ba zai iya ba, to bai gwada ba ne. Ni yanzu Ina da aure da yara, Ina aiki, Ina kasuwanci, kuma duk na iya. Ba dan komai ba, sai dan na sa a raina tabbas zan iya.

A wannan lokacin mata a nawa fahimtar ba su da lokacin cewa Ina aiki ba zan yi kasuwa ba, sabida sauyin rayuwa da aka samu. Yanzu duk yawan albashi buƙatar rayuwar ta fi shi girma. Kuma dole sai an jira wani ƙarshen wata. Ita kuma buƙata ba ta da lokaci, zuwa kawai ta ke. Ga wata rayuwa da ake ciki, ba kowa ke son baka aro ko bashi ba. To idan da albashin nan ka dogara za ka yi ta takaici da vacin rai.

To anan kin ga idan kana sana’a ka wuce wannan takaicin. Sannan maganar kula da iyali shi ma, komai tsara shi za ka yi yanda lokacin zai maka daidai. Musamman ma mu da muke ‘online Business’. Lokacin aiki daban, lokacin aikin gida daban, lokacin ɗaukar waya a yi kasuwanci daban.

Ta yaya ilimin ‘ya mace zai amfani mijinta da ‘ya’yanta?

Shi ilimi gishirin rayuwa ne. Kuma Annabi S. A. W ya ce, “ilimantar da ‘ya mace, kamar ilimantar da al’umma ne bakiɗaya.” Idan mace tana da ilimi hatta dabbobin gidanta ta san yanda za ta zauna da su lafiya ba ma iyalanta ba. Duk macen da ke da ilimi sai kin ga rayuwar gidanta daban, kamar ita ta tsarawa kanta.

Dukkan yawancin manyan malamanmu na addini za ki ji a hannun mahaifiyarsu suka fara karatu ko ita ta ɗora su kan tafarkin karatun. Misali duba tarihin Imam Malik da sauransu. Wannan kaɗai zai qara tabbatar maka da ilimin mace na da matuƙar tasiri da muhimmanci a rayuwar iyalinta. Duk gidan da aka samu mace mara ilimi sai kin tarar da shi ba yanda ake so ya kasance ba.

Wane kira za ki yi ga matasa kan bin sawun da ki ka taka kan tu’ammali da kafafen sada zumunta?

Kira na ga matasa shi ne, Ina faɗa, Ina ƙara faɗa wannan lokacin ba na zama ba ne. Rayuwa ƙara tsada ta ke, abubuwa a ƙasar nan ƙara runcavewa suke. Kar su dogara da sun yi digiri za su samu aikin gwamnati, dan akwai irinka dubu da suke jira, ko kuma su ce suna aiki suna da albashi ba za su yi sana’a ba. Arziki yana cikin kasuwanci, aikin gwamnati shi rufin asiri ne. A tashi a kama sana’a ko dan a tsira da mutumci.

Akwai mata masu zaman kashe wando, a naki hasashen me hakan ke nufi a rayuwarsu..?

A nan za mu dasa aya a wannan tattaunawa da muke yi da matashiya Jiddah Haulat Nguru. Da yardar mai dukka za mu kawo ƙarashin tattaunawar a sati mai zuwa, inda baƙuwar tamu zata soma da amsa mana tamkar da muka yi mata, kafin wasu tambayoyin.