Duk macen da ta dogara da miji, za ta kwashi haushi – Fatima Kaita

*Yawancin abinda ke jawo wa ‘ya’ya mata shiga harkar lalacewa na da alaƙa da rashin sana’a – Fatima

Daga AISHA ASAS

Fatima Kaita cikakkiyar ‘yar boko kuma ‘yar kasuwa sannan ‘yar gwagwarmayar siyasa, a hirar ta da jaridar Manhaja ta taɓo abubuwa da dama da su ka shafi muhimmancin sana’a ga ‘ya mace ta yadda ba sai ta rage murya a wajen maigida ko ‘yan’uwa ba. An dai ce waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi, don haka ga yadda hirar ta kasance:

Ko za ki faxa wa masu karatu sunan ki da kuma ɗan taƙaitaccen tarihin ki?
Assalamu alaikum, da farko dai suna na Fatima Abdullahi, amma da yawa sun fi sani na da Fatima Kaita. Kuma ni haifaffiyar Jihar Kaduna ce, a ƙaramar hukumar Zariya, amma na tashi a cikin Kaduna, wato Kaduna ta Arewa a Unguwar Hayin Banki. Na fara karatu tun daga Nursery, firamare har zuwa sakandare duk a Kaduna. Bayan kammala karatuna na sakandare ne na samu gurbin karatu a jami’ar Bayero ta Kano a shekarar 2009, na fara karantar ‘Industrial Chemistry’ amma cikin ikon Allah ban kammala ba na bar karatun dalilin yajin aiki da aka yi. Daga baya na koma makarantar ‘Shehu Idris College of Health Sciences and Technology Maƙarfi, Kaduna’. Nan na karanci ‘Medical Rehabilitation’, daga nan na koma makarantar ‘College of Health Sciences and Technology’ ta Tsafe da ke Jihar Zamfara inda na karanci ‘Medical Laboratory Technician’. A yanzu ina aiki da Kaduna State Ministry of Health, ina aiki a asibiti. Sannan ina ɗan taɓa harkar kasuwancin kayan kitchen, takalma, jakunkuna da kuma zannuwan gado. Babu wani abinda na sa a gaba a yanzu kamar samun cigaban rayuwata, ci gaba da karatu da kuma faɗaɗa sana’a ta. Sannan ina son ganin mata sun samu cigaba a kowane fanni na rayuwa kuma ana damawa da su a mutunce.

Ga shi ki na aikin gwamnati ki na kuma sana’a, shin mene ne muhimmancin sana’ar nan a wajen ‘ya mace musamman wacce ta ke ɗakin mijinta?
Gaskiya sana’a ga ‘ya mace babu abinda ya fi shi muhimmanci a rayuwarta. Saboda ita ce rufin asirinta, kuma kariya ga rayuwarta musamman idan ma ba ta yi aure ba. Domin mafi yawancin abinda ke jawo wa ‘ya’ya mata shiga harkar lalacewa na da alaƙa da rashin sana’a. Saboda idan mace ta na sana’a ta fi namiji ma amfanar da al’umma da kuma iyalinta. Sana’ar mace a ɗakin mijinta kuma ai ita ce ma kusan zaman auren, don mafi yawanci yanzu auren da ake yi auren ‘team work’ ne, wato taimake ni in taimake ka. Don mace mai sana’a ta na ba da gudummawa mai matuƙar yawa a wajen zamantakewar aure, hidimar ‘ya’ya da na ‘yan’uwa ma bakiɗaya.

Wasu mazan su na ƙorafin cewa sana’ar ‘ya mace musamman mai aure da ke ɗakin mijin ta ta na hana ta sauke haƙƙoƙin mijin ta da na ‘ya’yan ta, shin ya ki ke ganin wannan batu?
Gaskiya ba haka ba ne, ita macen ma ai saboda ta taimake shi ta ke sana’ar. Kuma mace mara kula ai musamman ce, ba lallai sai ta dalilin sana’a ba ne za ta zamo mai rashin kulawa da haƙƙoƙin miji. Wata dalilin sana’ar ne ma za ta rinƙa ririta mijinta.

Da jarin naira nawa ki ka fara sana’ar ki har ta kai ki ga bunƙasa haka?
(Dariya). Ai kin san shi jari sirri ne, amma Alhamdu lillah, na ɗan zuba abinda na san iya ƙarfi na ne kuma ban matsa wa kaina ba.

Idan a ce mace za ta zo wajen ki neman shawarar fara sana’a, shin wace sana’a za ki ce ta yi mai sauƙi da kuma samu wadda ba sai ta ajiye kuɗi masu yawa ba?
Ita ai sana’a kamar yadda na faɗa sirri ce da kuma sanin abinda ke ciki musamman akan sana’ar da za ka fara. Idan har zan fara sana’ar sayar da manja da jarin naira dubu goma, wata da jarin dubu biyar za ta fara kuma sai ka ga ta zama ta fini samun riba da kasuwa a sana’ar. Ba lallai ba ne jari ya zama ƙarfi ɗaya ba kafin mutum ya yi sana’a ba. Amma kowace sana’a dai abinda na sani ta na buƙatar jari.

A wane matsayi ki ka ajiye duk macen da ta tsaya dogaro da mijin ta ko wasu ‘yan’uwan ta kawai ba tare da ta tashi ta kama sana’a ba?
Gaskiya duk macen da ta dogara da cewa miji shi zai mata komai to lallai za ta kwashi haushi. Ai idan ta na neman zaman lafiya ma a gidan mijin na ta da farin ciki ta nemi sana’a. Mace mai sana’a ma ta fi daraja a idon namiji. Kuma ai ita sana’a ma rufin asiri ce.

Ko akwai wata gagarumar matsala da rashin tsafta ke haifar wa mace a gidan auren ta, musamman na zamantakewar aure a tsakanin ta da maigida?
Ai duk macen da ba ta da tsafta to bai kamata a saka ta a lissafin mata ba. Don ita mace ‘yar tsafta ce, da tsafta aka san mace, duk inda ka ga mace to ya kamata tsaftar ta ne zai zama ‘identity’ na ta. To balle a ce tsaftar gidan da ta ke zama da tsaftar jiki da na ‘ya’yan ta idan ta na da su. kin ga nan ne ya kamata a gani a san cewa lallai wannan wurin mace ke mulki a ciki. Amma da zarar ba ta tsaftace muhallin ta da jikin ta ba, to daga lokacin mijin ta zai fara ƙyamar ta, ya fara tunanin sake aure ko da bai da niyya; sannan rashin tsafta ta na kashe aure murus. Kuma ai ko a wane irin addini mace ke bi ta san matsayin tsafta a addinin. Tsafta kuma lafiya ce ta musamman mai zaman kanta.

Me ya fi faranta miki rai a harkokin kasuwancin ki?
Abinda ya fi faranta min rai shi ne idan na ba ka kaya in ga an ba ni kuɗi na cas a hannu, kuma in samu riba mai tsoka.

Waɗanne nasarori ki ka samu a rayuwar ki musamman ɓangaren sana’a?
Gaskiya Alhamdu lillah, babbar nasarar ma ita ce samun rufin asiri da kuma sanya wasu farin ciki a cikin rayuwar su.

Ƙalubale fa?
Ai kowane al’amari na rayuwa akwai ƙalubale, sai dai kawai ƙalubalen sana’ar mu ba ta wuce ta masu bashi ba. Kin san yanzu kusan kashi 90 cikin 100 na masu sayen kaya bashi su ke ɗauka. Kuma wajen biya a yi ta fama da su, wasu ma sun cinye kenan sai dai a lahira.

Shin Hajiya Fatima Kaita ta na taɓa siyasa ne, ko kuwa ma akwai wani matsayi da ki ke da burin tsayawa takara?
Eh, ina ɗan taɓawa, kuma ina da burin tsayawa takarar ‘yar majalisar jiha da yardar Allah.

Wace kala ki ka fi so a rayuwar ki?
Ina son ‘pink’ sosai, kin san shi ne kalar mata.

Wane abinci ya fi kwanta miki a rai wanda ba kya gajiya da cin shi?
Na fi son shinkafa, domin ko ƙazamiyar mace ta dafa sai na ci (dariya).

A cikin kayan itatuwa wanne ne ki ka fi son ci ko sha?
Ina bala’in son kankana, ayaba da kuma mangwaro idan lokacin shi ya yi.


Ana cewa ‘yan matan yanzu sun cika ruwan ido, sun fi karkata ga hamshaƙan masu kuɗi da motar hawa ta alfarma kafin su kula samari, shin da gaske ne wannan maganar?
(Dariya). Ai babu wanda ba ya son mai kuɗi, su ma mazan yanzu sun fi son mata ma su abin hannun su kuma hamshaƙai. Amma maganar gaskiya ita ce, ba kowace mace ba ce ta ke da wannan ra’ayin. Kawai dai mun yi qaurin suna ne saboda halin mafi yawan cikin mu hakan ne. Amma jam’in da ake mana ba a mana adalci.

To wace shawara za ki ba ‘yan mata wajen neman mijin aure?
Ina cikin su, shawara ita ce mu ji tsoron Allah kuma mu yi addu’ar samun miji mai tsoron Allah, mai tausayin mu. Sannan sai mun natsu, mun mutunta kan mu, mun kama kan mu kafin mu samu mazaje nagari.

Amsar ki ta zo a kan gaɓa, kenan dai Fatima Kaita ta na nufin ita ma ta na layin ‘yan mata?
Ƙwarai kuwa, ba ni da aure, mu na dai jiran lokaci kuma mu na fatan Allah ya kawo nagari.

Me ke saurin sa ki fushi?
Idan mutum ya yi min ƙarya ko sharri.


Wane abu ne ba za ki taɓa mantawa da shi ba a rayuwar ki, na mamaki, farin ciki ko al’ajabi?
Gaskiya mutuwar mahaifi na ita ce abinda ba zan taɓa mantawa da ita ba.

Ko akwai wani kira da za ki yi wa gwamnati na ganin ta tallafa wa mata da jari don bunƙasa sana’ar su?

To kullum ai ana wannan kiran, sai dai kawai in ƙara tini ga gwamnati cewa mata fa su ne kashi 80 cikin 100 na ma su ba su ƙuri’a a ko wane zaɓe. Sannan mata su ne ke tallafa wa gida ko da mai gida ba ya nan. Kuma su ne jigon kowace al’umma. Idan da gwamnati za ta tallafa wa mace ɗaya, macen nan za ta iya zama silar mata biyar su dogara da kan su. Kuma ci gaban kowace al’umma sai da mata. Don haka ya kamata gwamnati ta kula da sana’o’in da mata ke yi wajen ba su tallafi na kuɗi ko na kayan sana’ar ta su.

Wacce shawara za ki ba wa mata?
Ina kira ga ‘yan’uwa na mata da babbar murya da su tashi su nemi sana’a, su dage da neman sana’a don kuwa duk macen da ta ce za ta zauna a wannan marra za ta ga zaunau. Saboda haka mata a yi haƙuri, a tashi a kama sana’a.

Za mu so ki yi wa masu karatu ɗan tsokaci a kan haƙuri da rayuwa.
Haƙuri babban jigo ne a rayuwa, wallahi duk wanda ya yi haƙuri a rayuwa ba zai taɓa taɓewa ba, idan ka na mu’amala da mutane dole a ɓata maka rai, amma idan ka yi haƙuri sai ka ga ka cimma narasar da ba ka taɓa zato ba.

Me za ki ce wa jaridar Manhaja?
Toh ni dai ba ni da abin da zan ce wa wannan jaridar sai dai Ubangiji Allah ya sa ku fi haka, Allah ya kare ku ya kuma tsare ku daga sharrin masu sharri, na gode.